Shugaban ma'aikatan fadar gwamna da Kwamishinoni 9 sun yi murabus daga mukamansu a Delta

Shugaban ma'aikatan fadar gwamna da Kwamishinoni 9 sun yi murabus daga mukamansu a Delta

  • Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Delta, Ovie Agas, ya yi murabus daga kan kujerarsa kuma ba takara zai yi ba a 2023
  • Kwamishinan yaɗa labarai, Mista Aniagwu, ya ce sauran kwamishinoni 9 da hadimai sun yi haka ne saboda shiga takara
  • Gwamnan jihar, Okowa, ya sha alwashin cewa jam'iyyar PDP ba zata nuna wa wani ɗan takara banbanci ba

Delta - Shugaban ma'aikatan fadar gwamnan jihar Delta, Ovie Agas, tare da wasu kwamishinoni Tara sun yi murabus daga kan muƙamansu, kamar yadda Premium times ta rahoto.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Charles Aniagwu, shi ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai ranar Laraba a Asaba, babban birnin Delta.

Yace Murabus ɗin ya yi dai-dai da tanadin doka a sashi na 84 (12) a kundin dokokin zaɓen 2022 da ya yi magana kan masu riƙe da mukaman siyasa dake neman takara.

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

Gwamnan jihar Delta. Ifeanyi Okowa.
Shugaban ma'aikatan fadar gwamna da Kwamishinoni 9 sun yi murabus daga mukamansu a Delta Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Aniagwu ya bayyana cewa shugaban ma'aikata ya aje muƙaminsa ne domin samun damar yin aiki a matsayin wakili a wurin zaɓen wanda zai tabbatar da bin doka.

Kwamishinan ya kuma ce sauran kwamishinoni Tara da kuma hadimai sun yi murabus ne domin neman takara a kujeru daban-daban a zaɓen 2023.

Wane shiri PDP take a jihar Delta?

A ranar Talata da ta gabata, gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ya yi jawabi a taron PDP reshen Delta, inda ya tabbatar da cewa jam'iyya ba zata nuna wa yan takara banbanci ba a zaben fidda gwani.

Mista Aniagwu yace shugabannin PDP a jihar Delta suna aiki ba dare ba rana domin ganin an aiwatar da zabukan fidda gwani cikin kwanciyar hankali.

A cewarsa, akwai alaka mai kyau tsakanin tsohon gwamna, James Ibori, da kuma gwamna Okowa domin dukkan su sun halarci taron.

Kara karanta wannan

Wajibi ne APC ta lashe zabe a 2023 saboda ban taba rashin nasara ba, Abdullahi Adamu

A kalamansa, kwamishinan yaɗa labarai ya ce:

"A ranar Talata, jam'iyyarmu ta gana da manyan masu ruwa da tsaki da jagororinta a jiha."
"Gwamna da kuma shugaban jam'iyya sun yi jawabi kan bukatar kowane ɗan takara ya taka rawa mai kyau kuma ya tabbatar da ba'a samu hargitsi ba.

A wani labarin kuma Daga karshe, Gwamna Ortom ya fayyace yankin da PDP zata ba takarar shugaban ƙasa a 2023

Shugaban kwamitin karba-karba na jam'iyyar PDP ya musanta rahoton cewa sun buɗe kofa kowa ya nemi takara a zaɓen 2023.

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ya ce sun kammala aikinsu kuma sun kai wa NEC rahoto, wuƙa da nama na hannunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel