Da Ɗumi-Ɗumi: PDP Ta Sha Kaye a Kotu, An Ƙi Ƙwace Kujerar Gwamna Ayade Da Ya Koma Jam'iyyar APC

Da Ɗumi-Ɗumi: PDP Ta Sha Kaye a Kotu, An Ƙi Ƙwace Kujerar Gwamna Ayade Da Ya Koma Jam'iyyar APC

  • Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja ta fatattaki karar da PDP ta yi akan korar Gwamna Ben Ayade na Jihar Cross River da mataimakinsa daga mukamansu
  • Hakan ya biyo bayan sauya shekar da suka yi inda suka koma jam’iyyar APC duk da cewa lokacin suna PDP ne aka zabe su suka hau mukaman
  • Alkalin, Justice Taiwo Taiwo ya ce kotun ba ta da karfin da za ta iya korarsu, kundin tsarin mulki ne kadai zai iya korar gwamnan da mataimakinsa

Abuja - Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Alhamis, ta yi watsi da karar da jam'iyyar PDP ta shigar na neman kotun ta tsige Gwamna Ben Ayade na Jihar Cross Rivers da mataimakinsa Ivara Esu bayan sun koma jam'iyyar APC.

A hukuncin da Mai Shari'a Taiwo Taiwo ya yanke, ya ce ba za a iya kwace kujerun mutanen biyu ba sai dai kawai ta hanyoyin da ka lissafa a sashi na 180, 188 da 189 na kundin tsarin mulkin 1999, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Sojoji sun dakile mota dauke da N100m kudin fansa za'a kaiwa yan bindiga

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu Ta Ƙi Ƙwace Kujerar Gwamnan Ayade Da Mataimakinsa Saboda Koma Wa APC
Kotu Ta Ƙi Ƙwace Kujerar Gwamnan Ayade Da Mataimakinsa Saboda Koma Wa APC. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alkalin ya tsaya akan cewa sauya shekar gwamna ko mataimakinsa daga wata jam’iyya zuwa wata ba ta bayar da damar cire shi kamar yadda Vanguard ta bayyana.

Alkalin yace kotun ba ta da hurumin cire su daga mukamansu

Justice Taiwo ya tsaya akan cewa:

“Kundin tsarin mulki ne kadai zai iya sanyawa a cire wadanda ake kara na 3 da na 4. Kotun nan bata da damar da za ta cire su.”

PDP ta maka kara ta FHC/ABJ/CS/975/2021, inda ta bukaci a cire Ayade da mataimakinsa, ganin sun bar jam’iyyar da ta dauki nauyinsu har aka kara zabensu amma suka bar ta.

Har ila yau jam’iyyar ta bukaci kotun ta yi amfani da shashi na 221 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 wanda aka gyara da kuma salon mulkin demokradiyya, ta tsaya akan cewa duk kuru’u na jam’iyya ne ba na dan takara ba.

Kara karanta wannan

Najeriya na cikin wani hali: Tinubu ya ba wadanda harin 'yan bindiga na jirgin kasa ya shafa tallafin N50m

Duk a cikin takarda daya, PDP ta yi karar INEC da APC

Kuma ta bukaci kotu ta bai wa hukumar zabe ma zaman kanta, INEC, umarni akan ta yi gaggawar bai wa PDP damar kawo wasu daban wadanda zasu maye gurbin Ayade da Esu ko kuma ta shirya zaben gwamnoni na Jihar Cross River kamar yadda sashi na 177 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar, kuma kada ta ba su damar tsayawa takara bisa yadda kundin tsarin mulkin Najeriya, sashi na 192 (1) (b) ya tanadar.

Baya ga Ayade da mataimakinsa, PDP ta kai karar INEC da APC duk a takarda guda.

Ba A Ga Atiku Ba A Taron Da Wike Ya Yi Da Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar PDP

A wani labarin, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya bai halarci taron sirrn da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya shirya ba tare da wasu ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ba, yayin da zaben fidda gwanin jam’iyyar ya ke karatowa.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: PDP tayi watsi da tsarin karba-karba, tace kowa zai iya takaran kujeran shugaban kasa

An tattaro yadda ‘yan takarar suka dade suna tattaunawa dangane da wanda zai tsaya takara don gudun tashin tarzoma ta cikin jam’iyyar yayin zaben, The Nation ta ruwaito.

‘Yan takarar da suka halarci taron da aka yi gidan gwamnati da ke Port Harcourt sun hada da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed; Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon manajan darekta na bankin kasa da kasa na FSB, Dr. Mohammed Hayatu-Deen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel