Shugabancin 2023: Okorocha ya ce ya kamata Tinubu ya hakura ya bar masa tikitin APC

Shugabancin 2023: Okorocha ya ce ya kamata Tinubu ya hakura ya bar masa tikitin APC

  • Rochas Okorocha ya bayyana cewa shine ya fi cancanta a cikin dukkanin yan takarar shugaban kasa na APC
  • Okorocha wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Imo ya bayyana hakan ne a Eagles Square a ranar Asabar, 26 ga watan Maris
  • A cewarsa, jagoran jam’iyyar na kasa, Asiwaju Tinubu, zai janye masa domin ya gaji shugaba Buhari a 2023

AbujaRochas Okorocha, daya daga cikin masu neman kujerar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a zaben 2023, ya bayyana cewa zai lallashi babban jagoran jam’iyyar, Bola Tinubu domin ya janye masa wajen mallakar tikitin jam’iyyar.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Okorocha ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a wajen babban taron jam’iyyar na kasa da aka yi a Abuja.

Kara karanta wannan

An fitar da sunayen wadanda za su rike mukamai a APC, babu wasu ‘Yan takarar Buhari

Shugabancin 2023: Okorocha ya ce ya kamata Tinubu ya hakura ya bar masa tikitin APC
Shugabancin 2023: Okorocha ya ce ya kamata Tinubu ya hakura ya bar masa tikitin APC Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Tsohon gwamnan na jihar Imo ya bayyana cewa akwai yiwuwar shi da Tinubu ne za su iya zama manyan yan takara daga yankin kudancin kasar.

Ya ce:

“Kawu Tinubu da ni ne za mu iya zama manyan yan takara daga kudancin Najeriya. Na san cewa a lokacin da ya kamata, yana iya zama haka saboda shine yake kan gaba a kudu maso yamma sannan nine gaba a kudu maso gabas.
“Don haka bari mu ga abunda zai faru a tsakaninmu. Sannan idan hakan ya kasance, zan nemi ya dan sassauta domin mu kai wannan sashi gaba. Mutane na sona kuma ina ganin saboda sun yarda cewa ni mai kula ne, sun yarda ina so da tausayawa dan adam, sun yarda ni ba mai nuna kabilanci bane.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni ga masu sukar APC: Taron gangami ne a gabanmu, ba ta kowa muke ba

“Sun yarda ni ban san addini ko kabila ba, Musulmai, Kirista, Igbo ko Hausawa ko Yarbawa ba. Abun da nake gani shine mutum kuma wannan shine ya banbanci daga bangarena."

Okorocha ya bukaci yan Najeriya da su yi amfani da katunansu yadda ya kamata saboda yana da muhimmanci fiye da yadda suke zato. Ya kuma bayyana cewa 2023 zai basu damar yin zabi nagari.

Ya kara da cewa:

"Imma saboda dimokuradiyyar cikin gida ko na babban zabe, dole ne ku tabbatar kun kada kuri’ar ku daidai saboda katin zabe ya kunshi komai.
“Ilimin yaranku ne, lafiyarku ce, abinci da tsaron ku ne. Don haka ina shawartar mutane cewa darajar wannan kati a hannunku ya fi naira miliyan 100 don haka kar ku sayar da shi kan N10,000."

Gangamin taron APC: Buhari ya aika gagarumin sako ga Adamu, Omisore da sauran zababbun shugabanni

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci sabuwar zababbiyar uwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin Sanata Adamu Abdullahi da ta tabbatar da ganin cewa wadanda suka cancanta ne suka mallaki tikitin jam’iyyar a zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP

Buhari ya bukaci sabbin shugabannin da su inganta damokradiyyar cikin gida da daidaito sannan su tabbatar da ganin cewa ba’a yi cuwa-cuwa ba a zaben fidda gwanin jam’iyyar gabannin zaben 2023, rahoton Punch.

Da yake jawabi a babban taron gangamin jam’iyyar da aka yi a ranar Asabar, a Eagle Square Abuja, shugaban kasar ya kuma yi kira ga mambobin APC da su ci gaba da kasancewa a hade da karfi sannan su marawa sabon shugabancin jam’iyyar baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng