Wannan irin hadi haka! Martanin yan Najeriya bayan dan El-Rufai ya fitar da hoton mahaifinsa da Tinubu

Wannan irin hadi haka! Martanin yan Najeriya bayan dan El-Rufai ya fitar da hoton mahaifinsa da Tinubu

  • Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar hoton jagoran APC, Bola Tinubu da gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai
  • Wasu na ganin El-Rufai ma ya bi, inda wasu ke ganin shi za a tsayar a matsayin abokin takarar tsohon gwamnan na Lagas a 2023
  • Dan El-Rufai, Bello shine ya fitar da hoton wanda ya ja hankalin jama'a sosai

Yayin da ake tsaka da cece-kucen siyasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, wani hoton Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna zaune tare da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a shafin Twitter.

Dan gwamnan na jihar Kadunam Bello-El-Rufai ne ya wallafa hoton wanda ya samu martani daban-daban daga yan Najeriya a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

An fitar da sunayen wadanda za su rike mukamai a APC, babu wasu ‘Yan takarar Buhari

Wannan irin hadi haka! Martanin yan Najeriya bayan dan El-Rufai ya fitar da hoton mahaifinsa da Tinubu
Wannan irin hadi haka! Martanin yan Najeriya bayan dan El-Rufai ya fitar da hoton mahaifinsa da Tinubu Hoto: @B_ELRUFAI
Asali: Twitter

Tinubu, tsohon gwamnan jihar Lagas, ya ayyana aniyarsa ta son yin takarar kujerar shugaban kasa a babban zaben 2023.

Yayin da akalla gwamnoni uku suka fito suka ayyana goyon bayansu ga jigon na APC, Gwamna El-Rufai da wasu gwamnoni da dama a karkashin jam’iyyar basu fito sun nuna goyon bayan kowani dan takara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Saboda haka, wallafa hoton jagororin na APC biyu da Bello ya yi, ya haifar da rade-radi. Yayin da wasu ke kallon hoton a matsayin El-rufai na goyon bayan kudirin Tinubu, wasu na hasashen ko gwamnan na Kaduna na iya zama abokin takarar tsohon gwamnan na Lagas.

Shuraim Abubakar , @shuraim, ya rubuta:

“Da fatan ba wannan bane hadin a 2023.”

A martaninsa, Olajide Balogun,@olajt, ya rubuta:

"Shhh!!! Ku bari su ta cinka-cinka.”

A. A. Alhaji, @AZ_BinBaz, yace:

Kara karanta wannan

Bidiyon Wasu Matasa Suna 'Kaca-Kaca' Da Fuskar Tinubu a Hoto Ya Bazu a Dandalin Sada Zumunta

“Irin wannan hadi haka!!!"

#ThankASoldier, @DipoSpeak, ya ce:

“Wannan hadin zai yi ma’ana, wasu ba za su iya bacci ba daga yanzu, za su aiwatar da manufa da dama kuma zai yi fice. Muna lura sosai."

Dr. Ahmad, @Ahmad_ismaillll, ya ce:

"Wannan hadin zai yi kyau ga Najeriya BAT2023✔️"

TAH-LI-KAH, @freetalkerr, ya ce:

"Basa fada ne kuma????"

Bonaparte, @abba_mashasha, ya ce:

"A yanzu da aka kara elrufaiina cikin wannan tafiya ina fatan zai zaba mataimakin shugaban kasa 2027"

Hadimin El-Rufai Ya Koma Jam'iyyar PDP, Zai Yi Takarar Gwamna a 2023

A wani labari na daban, mun ji cewa Jimi Lawal, Mashawarci na muamman ga gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan habbaka saka hannun jari, ya shiga jam'iyyar PDP a Jihar Ogun., rahoton Daily Trust.

Lawal, wanda ya ziyarci sakatariyar PDP a Abeokuta, ranar Asabar, ya kuma ayyana niyarsa na yin takarar gwamna a zabe da ke tafe.

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamnan Kaduna: Abubuwa 6 nake son cimmawa idan na gaji El-Rufai

Ma'aikacin bankin da ya samu horaswa a Landan ya nemi kujerar gwamna a karkashin APC a zaben 2019, amma ya sha kaye hannun Gwamna Dapo Abiodun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng