Ni surukinku ne ku taimaka ku zaɓe ni, Ɗan takarar shugaban ƙasa ya roki deleget ɗin PDP

Ni surukinku ne ku taimaka ku zaɓe ni, Ɗan takarar shugaban ƙasa ya roki deleget ɗin PDP

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa, Bukola Saraki, ya roki Deleget ɗin PDP na jihar Ondo su zaɓe shi ko don kasancewarsa surukinsu
  • Tsohon shugaban majalisar dattawan, wanda matarsa yar Ondo ce, yace ba zai ci amana ba, zai cika duk alƙawarin da ya ɗauka
  • Shugaban PDP reshen jihar Ondo, ya bayyana Saraki da ɗansu, yace ba dalilin da zai hana su goyon bayansa

Ondo - Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma ɗan takarar shugaban kasa, Abubakar Bukola Saraki, ya roki deleget ɗin PDP na Ondo su taimaka su zaɓe shi.

Tsohon gwamnan jihar Kwara ya faɗa wa deleget ɗin su kaɗa masa kuri'unsu a zaɓen fidda gwani saboda shi surukinsu ne, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Daga karshe, Ministan Buhari ya yi faɗi shirinsa kan takarar shugaban ƙasa a 2023

Saraki, wanda ya tuna wa Deleget din cewa Mahaifiyar yar Owo ce yayin da matarsa kuma yar garin Ondo ce, ya ce idan ya zama shugaban ƙasa zasu amfana sosai.

Abubakar Bukola Saraki.
Ni surukinku ne ku taimaka ku zaɓe ni, Ɗan takarar shugaban ƙasa ya roki deleget ɗin PDP Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ɗan takarar ya kuma bayyana gwamnatin jam'iyyar APC mai ci da mara gaskiya kuma ta rusa tattalin arziƙin ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bukola Saraki, wanda ya samu wakilcin tsohon shugaban jam'iyyar PDP ta ƙasa, Alhaji Abubakar Baraje, ya ce shi ne mutum na farko da ya fara ankarar da badaƙalar dake cikin tallafin Man Fetur.

Ya kuma koka cewa kuɗin da ake biya na tallafin Man Fetur ya nunku sau uku karkashin mulkin jam'iyyar APC.

A kalamansa, ya ce:

"Mun zo nan ne saboda jihar Ondo ita ce babbar kalubalen mu. Mun san cewa Ondo ta Saraki ce, ba bu inda muka je Deleget ba su ce Saraki ne ɗan takararsu ba. Ɗan ku shi ne karshen matsalolin Najeriya."

Kara karanta wannan

Ana gab da babban taro, babban hadimin gwamnan APC ya yi murabus, ya fice daga jam'iyyar

"Yana da ƙarfin aikata abinda yake dai-dai, muna son ku tabbatar mana 100 bisa ɗari cewa Deleget ɗin Ondo zasu yi abun da ya dace, zasu zaɓi Saraki."
"Zai cika duk alƙawurran da ya ɗauka, ya yi an gani lokacin da yake shugaban majalisar dattawa kuma an ayyana shi shugaban da ya kafa tarihi."

Shin Saraki ya sami nasarar jawo hankalin su?

Shugaban PDP reshen jihar Ondo, Adams Fatai, ya kira Saraki ɗan jihar Ondo, ya ce Deleget ba su da wani dalili na kin goyon bayan Saraki.

Ya ce:

"Ya nuna banbancin mulki shiyasa ya samu nasara a shugabancin majalisar dattawa, ba zamu yi watsi da shi ba, Zubda jini ya yi yawa a Najeriya, muna bukatar wanda zai gyara."

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta gamu da cikas, Wani babban ƙusa tare da dandazon mambobi sun koma PDP

Jam'iyyar APC mai mulki ta gamu da wani cikas a Kwara yayin da take shirin babban gangamin taro na ƙasa ranar Asabar.

Kara karanta wannan

2023: Ku tsayar dani takarar shugaban kasa zan lallasa kowa a zabe, Gwamnan Arewa ya roki PDP

Tsohon ɗan takarar gwamna kuma jigo a APC ya jagoranci dandazon masoya sun koma jam'iyyar PDP mai hamayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel