Shugabancin APC na kasa: Mika kujera wata shiyya ba ka'ida bane, Abdulaziz Yari

Shugabancin APC na kasa: Mika kujera wata shiyya ba ka'ida bane, Abdulaziz Yari

  • Tsohon gwamnan Zamfara, Abdulazez Yari, ya ayyana cewa karba-karba ya saba kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC
  • Yari wanda ke neman kujerar shugabancin jam'iyyar mai mulki na kasa ya ci gaba da kamun kafa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar duk da mika tikitin yankin arewa ta tsakiya
  • Ya ce cancanta da kwarewa ya kamata a duba ba wai daga yankin da mutum ya fito ba

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdullazez Yari, ya ayyana cewa karba-karba ya saba kundin tsarin mulki a jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Yari ya kuma bayyana cewa shi ya riga ya siya fom din takarar kujerar shugaban jam’iyyar gabannin babban taron ranar Asabar, 26 ga watan Maris.

Leadership ta rahoto cewa Yari wanda ya bayyana hakan yayin da ya gana da masu ruwa da tsaki na APC a majalisar dattawa da kuma neman goyon bayansu, ya ce ya zama dole jam’iyyar ta samar da wanda zai iya.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Gwamna Tambuwal ya gana da IBB da Abdulsalami, ya bayyana shirin ‘yan takarar PDP

Shugabancin APC na kasa: Mika kujera wata shiyya ba ka'ida bane, Abdülaziz Yari
Shugabancin APC na kasa: Mika kujera wata shiyya ba ka'ida bane, Abdülaziz Yari Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Duk da cewar APC ta mika kujerar shugabancinta na kasa zuwa yankin arewa ta tsakiya, Yari ya ce yana bukatar goyon bayan sanatoci domin yin nasara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yari ya ce:

“Ina a nan domin neman bayanku kan kudirina na son zama shugaban APC na kasa. Kune masu ruwa da tsaki a wannan jam’iyyar da kuma alamar damokradiyya.
“Nan ne wuri na farko da nake kira tun da muka fara wannan tafiya a shekara daya da ta gabata. Zan so yin aiki tare da ku. Muna bukatar mutane da aka gwada kuma wadanda aka aminta da su.
“Mun san kundin tsarin mulkin jam’iyyar. Bai ware daga inda mutum ya fito ba kuma zan yi aiki tukuru don ganin na zama shugaba. Za mu yi aiki bisa tsarin mulkin jam’iyyar.
“Bai kamata takarar ya kasance game da inda mutum ya fito ba, ya kamata ya kasance game da abun da mutum zai iya. Muna fatan samar da shugaban kasa na gaba kuma muna bukatar shugaba da zai tabbatar da ganin cewa jam’iyyar ta ci gaba da nasara. Wannan zabe da muke ta dagawa ya kamata ace an yi shi tun shekara daya da ya wuce.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Najeriya ke son na tsaya takara, ba wai son raina bane, inji Atiku

“Na zo don gabatar maku da kaina da kuma neman goyon bayansu. Idan muka tsallake siradi, muna fatan yin aiki tukuru da samar da shugaban kasar nan na gaba.”

Yari ya kuma bukaci yan majalisar da su yi watsi da rade-radin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsayar da Sanata Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar na gaba, rahoton The Guardian.

Da yake mayar da martani, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, wanda ya tsaya a madadin shugaban majalisar ya ce Yari na daya daga cikin ‘yan takarar da suka ziyarce su a hukumance a majalisar tare da yin alkawarin mara masa baya.

Modu Sheriff ya janye daga takarar kujerar shugaban APC na kasa, ya bayyana dalili

A gefe guda, mun kawo a baya cewa, tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff ya janye daga takarar kujerar shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugabancin APC: Ɗan takara daga Zamfara ya janye kudirinsa awanni kafin tantancewa

Hakan na zuwa ne yan kwanaki kafin babban taron jam’iyyar mai mulki na kasa wanda za a yi a ranar Asabar mai zuwa.

A wata yar takaitacciyar hira a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris, a Abuja, Sheriff ya ce ya janye ne saboda tsarin rabon mukamai na jam’iyyar wacce ta mika kujerar zuwa ga yankin arewa ta tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng