2023: Kamata Ya Yi PDP Ta Nemi Gafara Daga Yan Najeriya, Ba Kuri'unsu Ba, Lawan

2023: Kamata Ya Yi PDP Ta Nemi Gafara Daga Yan Najeriya, Ba Kuri'unsu Ba, Lawan

  • Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce ya kamata babbar jam’iyyar adawa, PDP ta zagaye Najeriya tana neman yafiyar ‘yan Najeriya maimakon neman kuru’un su
  • A cewarsa, a shekaru 16 da PDP ta yi tana mulkar Najeriya ta lalata abubuwa da dama wadanda ya dace ta nemi yafiyar ‘yan Najeriya saboda su
  • Ya yi wannan maganar ne a Agasa, karamar hukumar Okene da ke Jihar Kogi yayin kaddamar da ayyukan Sanata Yakubu Oseni, mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya

Kogi - A ranar Alhamis Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce ya kamata babbar jam’iyyar adawa wato PDP ta zagaya kasa wurin neman yafiyar ‘yan Najeriya maimakon zagayen kamfen na neman kuri’u.

Lawan ya ce shekaru 16 da PDP ta yi tana mulki ta lalata kasa gaba daya, hakan yasa ya ce ya kamata ta nemi afuwa a wurin mutane ba kuru’un su ba,Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karar kwana: Jami'an kwana-kwana sun ciro gawar matashiyar da ta nutse a rijiya a Kano

2023: Kamata Ya Yi PDP Ta Nemi Gafara Daga Yan Najeriya, Ba Kuri'unsu Ba, Lawan
2023: Kamata Ya Yi PDP Ta Nemi Afuwa Daga Yan Najeriya, Ba Kuri'unsu Ba, Lawan. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Kamar yadda Lawan ya ce, 2022 shekarar cin gajiyar mulkin APC ne inda za a kaddamar da ayyukan da shugabanni suka yi kafin karshen shekarar.

Ya ce shekarar 2022 ita ce shekarar da za a kammala ayyuka da dama

Ya yi wannan maganar ne a Agasa, karamar hukumar Okene da ke Jihar Kogi yayin kaddamar da wasu ayyuka da Sanata Yakubu Oseni mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya a majalisar dattawa ya yi.

Kamar yadda Vanguard ta nuna, Lawan ya ce:

“Shekarar 2022 ta cin gajiyar mulkin APC ce a fadin Najeriya. Tun bayan zuwan jam’iyyar a 2015, ana ta ayyuka a kasar nan ciki har da gadar Neja ta biyu kuma da yardar Ubangiji a cikin wannan shekarar za a kammala sannan shugaban kasa da kan shi zai kaddamar.

Kara karanta wannan

Auran Sarauta: Sarkin Iwo zai angwance da jikar Sarkin Kano Ado Bayero, Firdausi

“Akwai titina da yawa da ake kan yi. An samu ci gaba mai yawa na ababen more rayuwa. A wannan shekarar kuwa da yardar Ubangiji za a kammala ayyuka kuma shugaba Muhammadu Buhari zai zagaye ko ina a kasar nan don kaddamar da ayyuka.
“Don haka za a ga ayyuka kwarai a wannan shekarar da APC ta yi. Babu wanda zai yaudari wani. Akwai mutanen da suka yi shekaru 16 suna mulki ba tare da tsinana wani abin a zo a gani ba. Mu kuwa cikin rabin shekaru 16 mun yi abinda basu iya yi ba.”

Jam’iyyar adawar ta nemi kuru’u a wurin ‘yan Najeriya kamar raina musu hankali ne

Ya ci gaba da cewa idan akwai abinda suke bukata a halin yanzu shi ne neman yafiyar ‘yan Najeriya maimakon neman kuri’un su.

Kamar yadda yace, idan suka bukaci kuri’u ‘yan Najeriya kamar sun raina mutane ne. Sun riga sun lalata kasar cikin shekaru 16, yanzu haka ana gyara abubuwan da suka bata ne.

Kara karanta wannan

Sabon rikicin APC: Buhari ya sanya mun albarka – Gwamnan Neja

A cewarsa, mulkin Shugaba Buhari zai kare ne a 2023 kuma ana sa ran kafin lokacin duk wasu ayyuka sun kammala wadanda ‘yan Najeriya za su gani su ji dadi.

Wannan mulkin yana iyakar kokarin ganin an ceto rayuwar ‘yan Najeriya. Zuwa karshen 2023 za a samu gyara a matsalolin tsaro a Najeriya. Za a samu gyara a ababen more rayuwa.

Lawan ya yi magana akan zaben da za ayi na 2023, inda yace za ayi zaben gaskiya da gaskiya. Kuma ana sa ran APC ce za ta lashe zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel