Karshen PDP a Kano da Arewa kenan: Shugaban PDP ya damu da ficewar Kwankwaso
- Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano ya bukaci manyan ‘yan jam’iyyar ta adawa da su tuntubi Rabiu Kwankwaso
- Kiran na shugaban PDP na jihar ya biyo bayan ficewar Kwankwaso da wasu manyan magoya bayansa daga PDP zuwa jam’iyyar NNPP
- A cewar shugaban, ana sa ran shugabannin jam’iyyar za su shawo kan Kwankwaso tare da jan hankalinsa ya ci gaba da zama a PDP
Jihar Kano - Da alamu dai ficewar tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Kwankwaso daga PDP ka iya haifar da damuwa tsakanin 'ya'yan jam'iyyar PDP a jihar.
Jaridar Tribune ta rawaito cewa shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Kano, Shehu Sagagi, ya ce barin Kwankwaso ya sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar NNPP babban kuskure ne.
Sagagi ya kuma yi kira ga manyan masu ruwa da tsaki na PDP da su tuntubi Kwankwaso domin jin matsalarsa da kuma neman hanyoyin magance su tun kafin lokaci ya kure.
A cewar Sagagi, yayin da PDP ta sami labarin cewa Kwankwaso zai fice daga cikinta, kamata ya yi ta aika da jakadan da ya dace domin a shawo kansa da kaucewa hakan.
Yadda PDP ta karya alkawarin da ta yiwa Kwankwaso
Da yake jawabi a wajen taron kamfen din takarar shugaban kasa na tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da wakilan PDP na Kano da Jigawa suka kai Kano, Sagagi ya ce Kwankwaso ya fusata ne a zaben shugaban PDP na shiyyar.
Ya yi zargin cewa an yi wa tsohon gwamnan alkawarin cewa za a ba shi dukkan foma-foman zaben a matsayinsa na shugaban jam’iyyar kuma mutum daya ne kawai za a bar shi ya tsaya takara.
Sai dai jam’iyyar ta karya alkawarin da ta dauka, inda ta sayar da fom ga wasu mutanen da ke cin dunduniyar jam’iyyar a Kano.
A kalamansa:
“Kuma maimakon jam’iyyar ta shawo kansa sai suka yi kamar ba abin da ya faru. Hakan ya sa ya sake duba matsayinsa a jam’iyyar.
“Idan aka bar shi ya tafi karshen jam’iyyar a Kano kenan da ma mafi yawan jihohin Arewa inda yake da magoya baya.”
2023: Kwankwasiyya da 'Yan kungiyar TMN za su narke a cikin jam'iyyar NNPP
A cikin kwanakin nan tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya kafa wata kungiyar siyasa, TNM, wanda a daren Litinin suka koma jam'iyyar NNPP.
NNPP tana daya daga cikin jam'iyyu masu rijista a kasar nan, Daily Trust ta ruwaito hakan.
Yayin zantawa bayan taron awa bakwai a Abuja, shugaban jam'iyyar TNM na rikon kwarya, AVM John Chris Ifeimeji (mai ritaya), ya ce, kungiyar ta yanke shawarar shigar da NNPP don ceto kasar daga mulkin kama karya da jam'iyyar mai mulki ke yi.
Daily Trust ta ruwaito cewa, an nada Ifeimeji a matsayin shugaban kwamitin kula da Jam'iyyar NNPP.
Babu wani aibu don mutum ya sauya sheka a siyasa - Kwankwaso
A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa shi bai ga wani aibu ba don yan siyasa sun sauya sheka daga wata jam’iyya zuwa wata, cewa hakan wani tsari ne na siyasa.
Kwankwaso ya bayyana cewa akwai hikima sosai idan dan siyasa ya sauya sheka zuwa wata jam’iyya domin gwada farin jininsa da kuma karbuwarsa a cikin mutane.
Dan siyasan ya bayyana hakan ne a Kano, a ranar Lahadi, 6 ga watan Maris, yayin wata ganawa da yan Kwankwasiyya da kuma jiga-jigan PDP a jihar a gidansa da ke Miller Road, Daily Trust ta rahoto.
Asali: Legit.ng