Saraki: Yadda kura-kuran PDP ya kawo Buhari kan karagar mulki

Saraki: Yadda kura-kuran PDP ya kawo Buhari kan karagar mulki

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya ce kuskuren PDP ne ya haifar da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Saraki ya ce a yanzu dabara ta rage ga jam'iyyar adawar ta kwato mulki daga hannun APC wacce yace bata da alkibla sai azabtar da yan kasar
  • Dan siyasar na daya daga cikin masu neman tikitin jam'iyyar PDP domin yin takarar shugabancin kasa a babban zaben 2023

Jigawa - Tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya alakanta hawan jamiyyar All Progressives Congress (APC) mulki da kura-kuran da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi.

Saraki ya bayyana matsayinsa ne ta hannun Farfesa Iyorwuese Hagher, shugaban kungiyar yakin neman shugabancinsa, lokacin da ya jagoranci tawagarsa zuwa Dutse don tattaunawa da masu ruwa da tsaki na PDP a jihar Jigawa, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Muna Da Huja Da Ke Nuna PDP Ce Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2019, in Ji Ayu

Saraki: Yadda kura-kuran PDP ya kawo Buhari kan karagar mulki
Saraki ya ce kuskuren PDP ne ya haifar da gwamnatin Buhari Hoto: BBC
Asali: UGC

Ya ce mafita kwaya daya da ya rage ma jam’iyyar adawar shine ta yi aiki don kwato shugabancin kasar a tsakiya domin kawo ainahin chanjin da kasar ke muradi.

Tsohon shugaban majalisar dattawan na daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a 2023, tare da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal da sauransu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hagher ya ce:

“Muna yarda cewa Najeriya ta cancanci shugaba da zai iya hada kanta.
“Muna sane kuma mun damu sosai da halin da kasar ke ciki a yau, ta yadda aka banzatar da hadin kanmu.
“Tattare da Bukola Saraki, mun ga shugaban kasa wanda ajandarsa itace inganta Najeriya, ta yadda banbancin kabila ko asali ba zai zama tushen shakku a tsakanin yan kasar ba.”

Ya yi takaici cewa saboda raunin PDP a 2015, yan Najeriya suka zabi APC, wacce bata da wata manufa ga kasar, inda ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari: Zaben 2023 zai fi kowane zabe zama sahihi saboda kokarin Buhari

“Da ace mambobin PDP basu karya martabarta ba da kuma hadewa da wasu kungiyoyi da suka zo suka kwace mulki, da APC bata taba mafarkin hawa mulki ba.
“Sun karbi mulki kuma muna iya ganin cewa basu da kowani ajanda sai dai azabtar da yan kasa.
“A yau babu wanda ya tsira, babu wanda ke murna saboda mune tushen talauci a duniya karkashin gwamnatin APC, mune kasa da ke da mafi yawan yara da basa zuwa makaranta, inda makomarmu ta zama wani iri.”

Dino Melaye ya dawo daga rakiyan Saraki, ya koma tafiyar Atiku

A wani labarin, mun ji cewa tsohon sanata wanda ya wakilci yankin Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Dino Melaye ya watsar da Abubakar Bukola Saraki inda ya koma bayan Atiku Abubakar.

A wani bidiyo da ke yawo, Melaye ya yi magana a wani taro da ya gudana tsakanin Atiku da wasu sanatoci a Abuja, inda ya bayyana dalilin da yasa yake bayan Atiku, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jigon PDP ga Matawalle: Ka daina tursasa mutane don kawai su shiga APC

Dino ya ce wasu takwarorinsa a majalisar dattawa suna ta al’ajabin dalilin da yasa yake bin Atiku alhalin tsohon ubangidansa na majalisar dattawa wato Saraki shima ya nuna sha'awarsa ga takarar kujerar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng