Ana yunkurin kawo doka saboda manyan majalisa su rika karbar fansho har su mutu

Ana yunkurin kawo doka saboda manyan majalisa su rika karbar fansho har su mutu

  • A yanzu ‘yan majalisa su na aikin yin kwaskwarima a kan kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999
  • Ana zargin cewa akwai makarkashiya da nufin a sa wa shugabannin majalisa fansho a dokar kasa
  • Idan aka yi wannan doka, shugabannin majalisa za su rika cin kudi duk shekara har su bar Duniya

Abuja - Wani sabon shiri da majalisar tarayya take yi zai ba shugabanninta dama su samu fansho na har abada. Jaridar nan ta Punch ta bankado wannan labari.

A kokarin garambawul da kwaskwarima da ake yi wa kundin tsarin mulki, shugabannin majalisar dattawa da na wakilai za su samu fansho har su mutu.

Idan aka amince da wannan garambawul a doka, Sanata Ahmad Lawan, Ovie Omo Agege da kuma Rt. Hon. Femi Gbajabiamila da Idris Wase za su amfana.

Kara karanta wannan

Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu

Tsakanin Laraba da Alhamis ake sa ran ‘yan majalisar wakilai za su yi zama a kan wannan batun.

Za a batar da biliyoyin kudi

The Cable ta ce wannan canji da ake kokarin kawowa yana cikin kare-karen da kwamiti suka yi wa kundin tsarin mulkin 1999, wanda zai jawo karin kashe kudi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A halin yanzu duk wani shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa da aka yi yana karbar miliyoyin kudi a shekara, wannan ya na ci wa gwamnati N7.8bn.

Femi Gbajabiamila
Shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

Sashe na 84(5) ya ba shugaban kasa da mataimakinsa dama su rika karbar fanshon muddin ba tsige su ko tunbukesu aka yi daga kan mulki saboda saba doka ba.

Allah wadaran wannan kudiri

Kungiyoyi sun fara yin Allah-wadai da wannan shiri da ‘yan majalisa suke yi, suka fara yin kira ga al’umma su fito su nuna ba za su amince da wannan doka ba.

Kara karanta wannan

Sakamakon zirga-zirgar Buhari: Kasar Ingila ta narka Naira Biliyan 5 domin inganta wuta

Wani babban jami’in kungiyar SERAP, Kola Dare ya yi hira da Punch, ya na mai sukar yunkurin da ake yi a majalisar, ya zargi shugabannin majalisar da son-kai.

Dare ya ce idan da gaske ne ana kokarin yi wa dokar kasa kwaskwarima saboda a cusa fanshon shugabannin majalisa, to ba kishin kasa aka yi la’akari da shi ba.

Yanzu haka irinsu SERAP su na shari’a da gwamnati a kan fanshon da ake biyan tsofaffin gwamnoni a jihohi. An dade ana kukan cewa akwai facakar kudi.

Majalisa ta yi magana a kan ASUU

Ana da labarin cewa Majalisar wakilan Najeriya ta tabo maganar yajin-aikin jan-kunnen da ake yi a jami’o’in gwamnnati a zaman farkon da tayi a makon nan.

Honarabul Dozie Nwankwo ya koka a game da yadda malaman jami’o’i suke shiga yajin-aiki bini-bini. An ci ma matsaya cewa majalisa za ta sa baki a kan batun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel