2023: Ta yuwu Najeriya ta samu 'yan takara 2 marasa amfani idan aka dubi yanki, Sanusi
- Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce akwai yuwuwar Najeriya ta tashi da 'yan takara 2 marasa amfani
- Tsohon gwamnan babban bankin Najeriyan, ya ce a halin yanzu Najeriya neman wanda zai mata aiki ta ke ba komai ba
- Khalifan Tijjaniyan ya tabbatar da cewa matukar aka gabatar da wanda zai kawo gyara a kasar nan daga kowanne yanki zai zabe shi
Muhammadu Sanusi II, tsohon sarkin Kano, ya ce alanta mulkin shugaban kasa ga yanki zai iya sa kasar nan ta kare da 'yan takara biyu marasa amfani a 2023.
A yayin jawabi a Arise TV a ranar Juma'a, Sanusi ya ce sau da yawa ya na kushe duk wata tattaunawa da za a yi kan yankin da ya dace ya samar da shugaban kasa, TheCable ta ruwaito.
Manyan jam'iyyu biyu na kasar nan na APC da PDP suna ta cece-kuce kan yankin da zai samar da shugaban kasa.
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya ce Najeriya ta na bukatar shugaban kasa wanda zai iya amfanar ta ba tare da duban yankinsa ba, TheCable ta wallafa.
"A koyaushe ina kushe wannan ra'ayin na cewa sai an mayar da hankali an ga inda shugaban kasa zai fito. Akwai gwamnonin kudu da ke cewa suna son shugabancin kasa da kuma gwamnonin arewa da ke cewa suna son arewa ta yi shugabancin kasa. Kun lura cewa babu wanda ya bayyana abinda ya ke so?" Yace.
"Duk wannan abun ana yin shi ne don killace shugabancin kasan zuwa wani yankin kasar kuma babban dodon zai bayyana. Hakan yasa a karshen al'amarin sai a kare a Najeriya ta fitar da 'yan takara biyu marasa amfani."
"Amma kuma, akwai manyan al'amura da ke gabanmu. Ga abu mai sauki salon bayyana zabe wanda aka shirya domin mayar da zaben a bayyane kuma cike da gaskiya, abun kunya suna cewa basu so, lamarin da ke nuna ana son magudi. Me yasa ba mu yin irin wannan maganar?
“Babban gazawar kasar nan bamu dubawa. Mun fi wayau idan aka yi batun kudi amma ba mu saka tunanin mu inda dace.
“Ku bani shugaban kasa daga kowanne yankin kasar nan wanda zai iya yin abinda ake so kuma za mu zabe shi. Ba shugabancin kasan zai dauka ya mayar kauyensu ba."
Benue: 'Yan bindiga sun halaka rayuka 2 a sabon farmaki
A wani labari na daban, iymagun 'yan bindiga sun halaka rayuka biyu a yankin Nyiev da ke karamar hukumar Guma ta jihar Benue.
Lamarin ya faru ne kusan kwana biyu bayan da aka kashe rayuka tara a wurare daban-daban na karamar hukumar, Daily Trust ta wallafa.
Shugaban karamar hukumar Guma ta jihar Benue, Caleb Aba, ya sanar da Daily Trust cewa, a ranar Alhamis 'yan bindigan suka zagaye yankin Nyiev kuma suka bude wa mazauna yankin wuta.
Asali: Legit.ng