2023: Tinubu ya naɗa ɗan shekaru 31 a matsayin shugaban watsa labaransa na ƙasa
- Yayin da zaben 2023 ke karatowa, jagoran jam’iyyar APC kuma mai neman takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya nada Kwamared Muhammad Mahmud a matsayin shugaban watsa labaransa na kasa
- Mahmud mai shekaru 31, dan asalin Jihar Borno, ya tabbatar wa manema labarai a Maiduguri cewa suna iyakar kokarin ganin sun tattaro jama’a, kwansu da kwarkwata wurin ganin burin Tinubu ya cika na maye gurbin Buhari
- A cewarsa, nadin nasa bai ba shi mamaki ba don salon mulkin Tinubu na daban ne, amma ya ce yana matukar farin ciki kuma zai tabbatar kwalliya ta biya kudin sabulu da yardar Ubangiji
Borno - Yayin da zaben shugaban kasa na 2023 yake karatowa, babban jagoran APC kuma mai neman takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada wani matashi dan asalin Jihar Borno, Kwamared Muhammad Mahmud a matsayin shugaban watsa labaransa na kasa, Vanguard ta ruwaito.
Yayin tattaunawa da manema labarai a Maiduguri, Mahmud ya ce zai tabbatar ya janyo hankalin mutane kwan su da kwarkwata wurin ganin sun ba Jagaban goyon baya don maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari da kuma dasawa daga ayyukan da ya tsaya na ci gaban kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mahmud ya ce nadin nasa bai ba shi mamaki ba saboda ya yarda da salon mulkin Tinubu wanda ba ya nuna bambancin yanki ko kabila.
A cewarsa, zai dage wurin jan hankalin jama’a don tabbatar da nufin Tinubu
Kamar yadda ya yi jawabin:
“Na amshi wannan kujerar ta shugaban kungiyar watsa labaran Tinubu.
“Babu tantama, wannan aikin zai taimaka wurin kamfen ga Tinubu wanda kowa ya san cewa jagora ne shi na kwarai.
“Don haka zamu jajirce wurin ganin nasara ta samu da yardar Allah da taimako, addu’o’i da goyon bayan ‘yan Najeriya.
Ku nemi kujerun sanatoci, ku bar matasa su shugabanci kasar - Tsohon ministan Buhari ga Atiku da Tinubu
“Kokarin mu ba zai tashi a tutar babu ba kuma ba za mu haddasa kiyayya ko gaba ba tsakanin junayen mu kamar yadda tsarin mu na tsawon shekaru yake.”
Ya ce Tinubu zai dasa daga inda Buhari ya tsaya wurin yaki da rashawa
Ya kara da cewa zasu bi salo da dabaru na musamman wurin jan hankalin jama’a ta kafafen sada zumunta, raba takardu da sauran su don tabbatar da manufar su.
A cewarsa, kamar yadda Vanguard ta nuna, babban burin su shi ne ganin mulki na kwarai ya samu da kuma ci gaban kasa irin na shugaban kasa Muhammadu Buhari karkashin inuwar APC.
Ya nuna farin cikin sa akan yadda aka yarda kuma aka amince da shi sannan aka nada shi wannan babban makamin.
A cewarsa, ba zai zauna ba har sai ya ga Jagaban ya samu nasarar lashe zabe don inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
Shugabancin ƙasa a 2023: Daga ƙarshe an bayyana inda Tinubu ya samo arzikinsa
A wani labarin, Shugaban Kungiyar Masu Goyon Bayan Tinubu, Abdulmumin Jibrin, tsohon dan majalisa wakilai na tarayya ya yi wasu muhimman bayanai game da arzikin tsohon gwamnan na Legas.
A hirar da aka yi da shi a TVC News, an sake yi wa Jibrin, tsohon Dan Majalisar Wakilai tambaya game da inda Tinubu ke samun arzikin.
Asali: Legit.ng