Rikicin siyasar Gombe: 'Yan sanda sun gargadi 'yan APC da PDP kan tada zaune tsaye

Rikicin siyasar Gombe: 'Yan sanda sun gargadi 'yan APC da PDP kan tada zaune tsaye

  • Yayin da siyasar Gombe ta yi kamari, rundunar 'yan sanda ta bayyana gargadi ga 'yan siyasar jihar baki daya
  • Ta shaida cewa, a yanzu ba lokacin yakin neman zabe bane, don haka ya kamata kowace jam'iyya ta kama kanta
  • Rundunar ta kuma gargadi iyaye kan barin 'ya'yansu cikin masu farmakar dukiyoyin jama'a da bangan siyasa

Jihar Gombe - Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta yi kakkausar gargadi ga jam’iyyun siyasa a jihar Gombe, inda ta bukace su da su daina duk wani nau’i na ayyukan da za su iya saba wa jadawalin yakin neman zabe.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ishola Babaita ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jihar, Punch ta ruwaito.

Siyasar jihar Gombe
Rikicin siyasar Gombe: 'Yan sanda sun yi martani kan fitinar da ke tsakanin 'yan APC da PDP | Hoto: leadership.ng
Asali: Facebook

Ya yi Allah-wadai da kone-konen rumfar APC da sakatariyar PDP da ofishin yakin neman zaben Atiku, da ke kan titin Gombe/Bauchi.

Kara karanta wannan

Takarar Atiku na rawa: Jagoran kamfen dinsa a arewa maso gabas da sauransu sun koma tsagin APC

Yayin da rundunar ke kira ga jam’iyyun siyasa da su guji tada hankali, ‘yan sanda sun bukaci iyaye da su sanya ido a kan ayyukan 'ya'yansu domin kada su kasance cikin masu tada hankula.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Babaita:

“Rundunar tana amfani da wannan kafar don fadakar da kowane mutum ko gungun mutane da su sani cewa lokacin yakin neman zabe bai zo ba tukuna.
“Duk bangarorin da abin ya shafa su natsu su kasance masu bin doka da oda tare da bayar da hadin kai ga rundunar yayin da ake kokarin bankado wadanda ke da hannu a wannan danyen aikin.
“A karshe rundunar ‘yan sandan tana nasiha ga daukacin jama’a da kuma mutanen jihar Gombe da su gargadi 'ya'yansu da su yi hattara da ‘yan siyasa da za su yaudare su su mai da‘ yan bangar siyasa."

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: Ganduje ya sake martani kan kisan Hanifa, ya ce dole ne a yi adalci

Hadimin gwamnan Arewa da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun yi murabus

Rikicin jam'iyyar APC reshen jihar Gombe ya dauki wani sabon salo ranar Laraba da daddare yayin da manyan jiga-jigan jam'iyya suka yi murabus.

The Nation ta rahoto cewa wadanda suka yi murabus daga APC ɗin sun hada da, tsohon kwamishinan lafiya, Dakta Ahmed Gana, mai baiwa gwamna shawara, Dijjatu Bappa, da babban jigo Jamil Isyaka Gwamna.

Murabus da ficewa daga APC na Bappa da kuma Gwamna ya biyo bayan sauya shekar Dakta Ahmed Gana zuwa jam'iyyar PDP mai hamayya kwana biyu da suka shude.

Bappa, a wata takarda da ta aike wa gwamnan mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Fabrairu, tace ta yi murabus nan take.

A wani labarin, gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC na kasa, Mai Mala Buni ya hadu da ‘yan tawayen APC na jihar Kano.

Kara karanta wannan

2023: Zan kawar da karuwai idan nayi nasara a zabe, Dan takaran shugaban kasa yayi alkawari

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Mai Mala Buni ya yi zama da jagororin jam’iyyar ta APC mai mulki na reshen jihar Kano a yammacin Talata a Abuja.

Kawo yanzu ba mu samu labarin matsayar da aka cin ma bayan wannan tattaunawa da aka yi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.