Atiku Abubakar ya bayyana lokacin da zai ayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023

Atiku Abubakar ya bayyana lokacin da zai ayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubabar, yace ba da jimawa ba zai fito ya bayyana shiga takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023
  • Atiku ya kai ziyarar jaje ga gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, bisa karuwar hare-haren yan bindiga a jiharsa
  • Yace yana cigaba da shirye-shirye amma zai bayyana wa yan Najeriya kudirinsa a lokacin da ya dace

Niger - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai sanar da shiga tseren kujerar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa lokacin da ya dace.

TVC News ta rahoto cewa Tsohon mataimakin shugaban ya faɗi haka ne bayan ganawa da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, a fadar gwamnatin jihar dake Minna, ranar Talata.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar ya bayyana lokacin da zai ayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: Atiku Abubakar/Facebook
Asali: Facebook

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan fito wa daga ganawar sirri da gwamna Abubakar Bello, Atiku yace yana jiran lokacin da ya dace kuma nan ba jimawa zai bayyana shiga tseren takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Atiku ya kai ziyara wajen tsohon shugaba IBB

Haka nan kuma, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019 ya jajantawa gwamnatin jihar Neja bisa hare-haren da yan bindiga suka kai wasu yankuna kwanan nan.

Atiku ya kuma bayyana cewa matsalar tsaron dake addabar jihar Neja da ma sauran jihohi na bukatar a maida hankali cikin gaggawa.

Punch ta rahoto Atiku yace:

"Yanayin tsaro a jihar Neja abin damuwa ne matuƙa, yanzun na gama gana wa da gwamna kuma tabbas yanayin ya zama abin damuwa."

Takarar Atiku zuwa yau

Atiku ya jima yana fito wa neman kujerar shugaban ƙasa tun bayan saukarsu daga mulki a matsayin mataimakin shugaba a shekarar 2007.

A shekarar 2015, ya fatata a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APC, amma ya sha ƙasa a hannun shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya samu nasara a zaɓe.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa zai fara neman shawara kan ko ya cancanta ya nemi takarar shugaban ƙasa a 2023

Sai dai, Atiku ya samu nasarar samun tikitin takara karkashin inuwar jam'iyyar PDP, amma ya gaza kai bantensa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2019.

Majalisa ta maida Poly zuwa Jami'a a arewa

A wani labarin na daban kuma Majalisar Dattawa ta ɗaga darajar kwalejin fasaha zuwa jami'a a Arewa

Majalisar dattawa ta amince da manyan muhimman kudirori da suka shafi makarantun gaba da sakandire a Najeriya.

A zamanta na yau Talata, Sanatocin sun amince da ɗaga darajar kwalejin fasaha zuwa jami'a a jihar Kwara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel