Da Dumi-Dumi: Sanatan APC ya sanar da kudirinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023
- Sanata a jam'iyyar APC, Sanata Rochas Okorocha, ya sanar da majalisar dattawa kudirinsa na neman ɗarewa kujerar shugaban ƙasa a 2023
- Tsohon gwamnan jihar Imo, a wata wasika da ya tura wa shugaban majalisa, yace zai gudanar da taron manema labarai na duniya kan manufarsa
- Ya ce yan Najeriya na bukatar nagartaccen shugaba da zai iya shawo kan matsalolin da suka addabi ƙasa
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Punch ta rahoto cewa Okorocha ya bayyana haka ne a wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya karanta a zaman yau Laraba.
A ranar Litinin, 31 ga watan Janairu, 2022, tsohon gwamnan zai yi jawabi a wurin taron manema labarai na duniya, inda ake sa ran zai yi ƙarin haske kan manufofinsa.
A wasikar, The Nation ta rahoto Sanata Okorocha yace:
"Kamar yadda kuka sani, hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta fitar da jadawalin zaɓen 2023, wanda ya haɗa da na ofishin shugaban tarayyan Nigeria."
"Yayin da zaɓen ke kara matsowa kullum kwana, yan Najeriya sun damu kan mutumin da zai rike musu amanar ƙasa. Wanda zai iya magance musu abin da ya hana su bacci."
Nagartar da ake bukatar shugaba na gaba ya tattara
Tsohon gwamnan ya zayyano wasu nagarta da yan Najeriya ke son wanda zai jagorance su a zabe na gaba ya tattara su, wanda ya haɗa da;
"Ɗan Najeriyan da ba ruwan shi da banbancin kabila, wanda zai iya haɗa kan ƙasa wuri ɗaya. Mutumin da yake da zuciyar tausayi da zai kula da talakawa, da masu rauni."
"Shugaban da zai iya samar da hanyoyin arziki ga yan ƙasa, ta hanyar warware matsalolin talauci, rashin tsaro da zaman kashe wandon matasa."
"Sakamakon haka zan kira gagarumin taron manema labarai na duniya kan kudirina na neman ofishin shugaban ƙasa a Najeriya. Ina rokon addu'o'in ku da fatan alkairi."
A wani labarin na daban kuma Pantami ya faɗi babban abinda yan bindiga ke amfani da shi wajen ayyukan ta'addanci a Arewa
Minsitan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami, yace yan bindiga na ribatar yawan faɗin kasa a jihohin arewa maso gabas wajen aikata ta'addanci.
Sheikh Pantami yace hudu daga cikin jihohin Najeriya shida da suka fi faɗi duk suna yankin arewa maso gabas.
Asali: Legit.ng