Janar Abdulsalami: Na faɗa wa Obasanjo kada ya shiga siyasa

Janar Abdulsalami: Na faɗa wa Obasanjo kada ya shiga siyasa

  • Janar Abdulsalami Abubakar (mai murabus), tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya ya musanta cewa shi ya ingiza Obasanjo ya shiga siyasa
  • Abdulsami ya ce, akasin hakan, shi ya shawarci Obasanjo ya tafi gida ya kula da lafiyarsa ne lokacin da ya zo wurinsa neman shawarar shiga siyasa
  • Ya ce Obasanjo ya masa godiya ya tafi amma kwatsam kawai sai ya ji sunan Obasanjo cikin masu takarar neman shugabancin kasa

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) ya bayyana yadda ya shawarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kada ya shiga siyasa bayan jim kadan bayan sako shi daga gidan yari.

Obasanjo, wanda gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha ta tsare, ya samu yanci ne bayan da Abdulsalami ya hau mulki, rahoton Daily Trust.

Janar Abdulsami: Na faɗa wa Obasanjo kada ya shiga siyasa
Janar Abdulsami ya ce ya shawarci Obasanjo kada ya shiga siyasa. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Abdulsalami: Rawar da Babagana Kingibe ya taka bayan mutuwar MKO Abiola

Daga bisani, Abdulsalami ya mika mulki da Obasanjo bayan an zabe shi shugaban kasa a 1999.

Bayan hakan, wasu masu suka sun zargi Abdulsalami da kakabawa 'yan Najeriya, Obasanjo, Janar din soja mai murabus a matsayin shugaban kasa.

Amma a hirar da aka yi da shi a Trust TV, Abdulsalami ya karyata hakan, inda ya bada labarin yadda jim kadin bayan sakinsa ya shawarci Obasanjo kada ya shiga siyasa.

Shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa ya ce ya shawarci Obasanjo kada ya shiga siyasa, a maimakon hakan ya tafi gida ya kula da lafiyarsa.

Ya ce ba shi da hannu cikin takarar Obasanjo da zamansa shugaban kasa a 1999.

Kalamansa:

"Shi (Obasanjo) ya zo ya gan ni don ya fada min cewa wasu kungiyar mutane sun zo sun same shi suna son su bashi tikicin takarar shugaban kasa."

Kara karanta wannan

"Siyasa ba zai taɓa fita daga jinin ka ba" - Shugaban PDP ya mayarwa Obasanjo martani

"Na ce masa, Sir, idan da nine kai, ka rabu da su. Sir, ka tafi gida ka kula da lafiyarka da sauransu. Ya ce, 'toh, Janar na gode da shawarar ka, zan sake tuntubar ka. Bai sake dawowa ba. Abin da na ji kawai shine yana daya daga cikin yan takarar shugaban kasa.
"Na yi kokarin fada wa mutane cewa babu hannu na a takarar Obasanjo. Duk abin da ya faru tsakanin su da jam'iyyun siyasa da wasu."

Abdulsalami ya kara da cewa ya bashi tallafi kamar yadda ya bawa sauran fursunonin domin su samu su murmure amma hakan baya nufin ya taimaka masa shiga takara ko zabe.

2023: Tsohon hadimin Atiku ya 'soki' Saraki da Tambuwal kan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

A wani labarin, Jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Ogun, Segun Showunmi a ranar Juma’a ya kalubalanci tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr Bukola Saraki da gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal akan tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba zan taba komawa jam'iyyarku ba, Obasanjo ya bayyanawa jiga-jigan PDP

A cewar Showunmi wanda tsohon kakakin dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019, Atiku Abubakar ne, Tambuwal da Saraki ba sa da gogewar da za su iya mulkar cukurkudaddiyar kasa kamar Najeriya.

Ya tsaya akan cewa Atiku ne kadai wanda ya fi dacewa ya tsaya takarar a PDP kuma ya lashe zaben 2023 da ke karatowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164