Dalilin da ya sa zan nemi takarar kujerar Buhari a 2023 – Tsohon gwamnan Zamfara

Dalilin da ya sa zan nemi takarar kujerar Buhari a 2023 – Tsohon gwamnan Zamfara

  • Sanata Ahmed Sani Yarima, ya kaddamar da aniyarsa ta son yin takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023
  • Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya ce zai yi takarar ne saboda shugaban kasa Buhari ya cike wa'adinsa wanda dama saboda shi ne ya ki yin takara tun a baya
  • Yariman Bakura ya kuma sha alwashin yakar talauci da jahilci idan ya zama shugaban kasar

Zamfara - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yarima, ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben 2023 mai zuwa.

Yarima wanda ya kuma kasance jigon jam'iyyar APC, ya ce zai yi takara ne saboda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala wa'adin mulkinsa.

A hira da ya yi da BBC Hausa, ya kuma bayyana cewa idan har ya zama shugaban kasar Najeriya zai yaki talauci da jahilci, domin a cewarsa sune matsalolin da ke damun kasar.

Kara karanta wannan

Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023

Dalilin da ya sa zan nemi takarar kujerar Buhari a 2023 – Tsohon gwamnan Zamfara
Dalilin da ya sa zan nemi takarar kujerar Buhari a 2023 – Tsohon gwamnan Zamfara Hoto: Thisday
Asali: UGC

Ya ce:

"Idan Allah ya raya mu zan tsaya takarar shugaban kasa a shekara ta 2023. 2007 na fito takara amma dattijan arewa karkashin kungiyar ACF da kuma manya-manyan yan arewa suka ce duk mu yan arewa mu janyewa Muhammadu Buhari, sai muka jaye masa.
"Kuma a wannan lokaci idan mutane za su tuna, da na hau mambarin jawabi, na yi alkawari muddin yana neman takara ba za a ganni na ja da shi ba. Shiyasa a 2017 nace idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai yi ba zan yi, amma muddin yana takara ba zan yi ba.
"Don haka yanzu Alhamdulillahi an zabe shi shugaban kasa a karo na biyu, kuma zai kare mulkinsa a 2023, don haka na bayyanawa jama'a cewa In shaa Allahu nima na fito takara in nemi shugabancin Najeriya idan Allah ya nufa."

Kara karanta wannan

Orji Kalu: Duk inyamurin da ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 bai san me yake ba

Kan dalilin da yasa ya nace sai ya shugabancin Najeriya, Yarima ya ce:

"Na yi mulkin Zamfara shekara takwas, na yi sanata shekara 12, na san cewa a wannan zaman da na yi cikin gwamnati, na gano matsalolin yan Najeriya da kuma Najeriya.
"Wannan kasa tana da matsala guda biyu 'talauci da jahilci'. Idan aka samu gwamnati da ta fito da tsare-tsare ta fannin noma da kiwo, fannin kasuwanci, fannin ilimi, inda za a yaki jahilci da talauci. Kowa yana da abun da zai yi, ina tabbatar maku za a samu zaman lafiya, tsaro zai tabbata a wannan kasa, mutane za su samu kwanciyar hankali.
"Duk wani abu da ka ga ana yi na ta'addanci, rashin abin yi ne da kuma jahilci."

Kan cewa zai yi wuya ya samu tikitin takarar APC kasancewar ya fito daga yanki guda da Buhari sai dan siyasar ya ce:

"Idan mutum yana cewa yana so ya yi maganar siyasa, abun da zai fara dubawa shine tsarin mulki na Najeriya da jam'iyya.

Kara karanta wannan

Garba Shehu: Buhari ya karya lagon rashawa shi yasa 'yan siyasa ke jin haushinsa

"A tsarin mulkin jam'iyyarmu APC, babu wani abu karba-karba. A tsarin mulkin Najeriya, inda duk ake takara za ka ji ana dan Najeriya, don haka ni dan Najeriya ne, maganar cewa na fito daga yanki daya da shugaba Muhammadu Buhari, idan ka lura, inda an fito cikin tsarin mulki ko ta doka ta kasa ance daga wannan jaha ta yi sai wannan jaha ko daga wannan yanki sai wannan, haukace ga mutum ya zo ya ce zai yi idan ba yankinsu bane za ta yi."

Magana ta canza: Sanatan APC ya ce yanzu da shi za a nemi takarar Shugaban kasa a 2023

A gefe guda, Orji Uzor Kalu yana cewa a baya ya fadawa irinsu Sanata Anyim Pius Anyim da David Umahi cewa ba zai nemi shugabancin kasa ba.

Amma da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Silverbird Television a ranar Juma’a, 21 ga watan Junairu 2022, Sanatan ya ce ya canza shawara a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Dan Shehu Dahiru Bauchi ya fito takarar shugaban kasa na 2023

A cewar Orji Uzor Kalu, mutane daga duka bangarorin kasar nan sun same shi, sun kuma roke shi ya fito neman titikin takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng