Osinbajo ya bada labarin yadda ya zama Mataimakin Buhari lokacin ba a san shi ba

Osinbajo ya bada labarin yadda ya zama Mataimakin Buhari lokacin ba a san shi ba

  • A watan Disamban shekarar 2021 Yemi Osinbajo ya bada labarin zamansa mataimakin shugaban kasa
  • Farfesa Yemi Osinbajo yace ikon Ubangiji ne kawai ya sa ya zama Mataimakin Najeriya a zaben 2015
  • Mataimakin shugaban kasar ya ce a lokacin da aka zabe shi, ba zai iya cin zabe a karamar hukuma ba

A yayin da batun yakin neman zaben 2023 ya fara kamari, an dauko wani bidiyon Farfesa Yemi Osinbajo ya na bayanin yadda ya hau kan karagar mulki.

A wannan bidiyo da ya ke kan shafin Facebook, an ji Yemi Osinbajo yana bada labarin abin da ya faru da ya ziyarci cocin The Restoration Life Assembly Int'l.

Mataimakin shugaban kasar ya ziyarci cocin The Restoration Life Assembly Int’l ne a lokacin da ya gana da limaminsu, Rabaren Dr. Udochi M Odikanwa.

Kara karanta wannan

Babu wanda ya fi Tinubu dacewa a 2023 – Tsohon Gwamnan Arewa ya kawo karfafan dalilai

Mataimakin shugaban kasar ya ce ya samu takara a jam’iyyar APC har ya hau kujerar da yake kai a yau ne saboda Ubangiji dai ya tsara zai rike mukamin.

Da yake yi wa mabiya jawabi a cocin, Farfesan shari’an ya ce a lokacin da ya samu daukakar, ba zai iya lashe ko da zaben shugaban karamar hukuma ba.

“Babu wanda zai samu wani abu face daga wajen Ubangiji ne. Shi ne yake azurta bawa da duk abin da ya samu. Duk wata kyauta daga gare Shi ne.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ubangiji ne yake yin komai da komai. Abin ba a karfi ko zafin neman mutum ba ne.” - Yemi Osinbajo
Osinbajo
Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: Professor Yemi Osinbajo Daga: Facebook
Asali: Facebook

“Idan lokaci ya yi, kuma an tsaga da rabonka, shi kenan. Ubangiji ya tsara komai, ya nufa ga shi yau ina kan kujerar mataimakin shugaban Najeriya.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya yi magana kan magajin Buhari

“Ba zan iya lashe ko zaben shugaban karamar hukuma a 2014 ba, ba zai yiwu ba. Babu wanda ya san da zama na, babu wanda ya san ko wanene ni.”
“Eh, na taba rike kujerar kwamishina a gwamnatin jihar Legas, amma an yi kwamishinoni birjik.”
“Babu wanda ya san ni, amma Ubangiji ya tsara sai na yi. A lokacin da aka zabe ni in zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa, ina shirin zuwa kotu.”
“Ina otel tare da abokan aikina, mu na shirya kara da za mu shigar a kotun koli washegari.”

- Yemi Osinbajo

Kwatsam sai Osinbajo ya ji kira a waya, aka tambayi inda yake domin a zo a dauke shi, daga nan sai ya ji an zabe shi ya yi takarar mataimakin shugaban kasa.

“Na san wannan lamarin Ubangiji ne, abin ba karfin mutum mutum ba ne. Ubangiji ya kuma sa ni a kujerar ne saboda wani dalilin da shi ya sani.” - Osinbajo

Kara karanta wannan

Umahi ga 'yan Najeriya: Bai kamata kuke tsoron inyamuri ya zama shugaban kasa a 2023 ba

Kudirin dokar zabe

Daga dawowa aiki bayan an yi hutun karshen shekara, sai aka ji cewa Gwamnoni sun ba ‘Yan majalisa shawarar su tuburewa matakin da shugaban kasa ya dauka.

Gwamnoni sun fadawa ‘yan majalisar tarayyar su kewayo da kudirin zaben da aka yi fatali da shi, ta yadda zai zama doka ko da shugaba Muhammadu Buhari bai so ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel