Dattawan arewa sun bayyana manyan sharudda 3 don marawa yan takarar shugaban kasa baya a 2023
- Kungiyar dattawan arewa ta bayyana wasu abubuwa da za ta duba kafin ta marawa yan takarar shugaban kasa baya a zaben 2023
- Kungiyar ta ce za ta duba kwarewa, mutunci da kuma jajircewar yan takara wajen bin doka da oda kafin ta mara masu baya a babban zaben kasar mai zuwa
- Ta kuma ce arewa na da yancin yin takarar shugaban kasa a zaben kamar kowani yankin kasar
Kaduna - Gabannin babban zaben 2023, kungiyar dattawan arewa ta ce yan Najeriya na da yanci iri daya domin yin takarar kujerar shugaban kasa.
Kungiyar a ranar Asabar, 15 ga watan Janairu, ta kuma kaddamar da cewar yan arewa kamar sauran yankunan kasar suna da yanci a zaben shugaban kasa na gaba.

Asali: UGC
A wata sanarwa da suka fitar a karshen taronsu a jihar Kaduna, dattawan na arewa sun jero muhimman abubuwan da za su yi amfani da shi wajen marawa shugaban Najeriya na gaba baya.
A cewar jaridar The Nation, sharuddan da ya zama dole yan takarar shugaban kasa na 2023 su cike sun hada da:
1. Kwarewa
2. Shaidar mutuncin mutum
3. Jajircewa wajen bin doka da oda
Ba zamu sake kuskuren zaben mutum irin Buhari ba, Dattawan Arewa
A gefe guda, mun kawo a baya cewa kungiyar dattawan Arewa ta bayyana cewa yankin Arewa zata zabi dan takaran shugaban kasa mai ikon sauya lamuran tattalin arzikin kasar da tsaro ba tare da la'akari da yankin da ya fito ba.

Kara karanta wannan
Umahi ga 'yan Najeriya: Bai kamata kuke tsoron inyamuri ya zama shugaban kasa a 2023 ba
Dattawan sun ce ba zasu sake zaben dan takara bisa kabilanci kamar yadda suka zabi Shugaba Muhammadu Buhari a 2015 ba.
Dattawan sun bayyana cewa Shugaba Buhari abin kunya ne ga Arewa da Najeriya gaba daya.
Asali: Legit.ng