Yan siyasar kudu maso gabas 5 da ake sa ran za su fafata a zaben shugaban kasa a 2023

Yan siyasar kudu maso gabas 5 da ake sa ran za su fafata a zaben shugaban kasa a 2023

  • Ana ta kira ga manyan jam'iyyun siyasar kasar a kan su mika tikitin takarar shugaban kasarsu ga yankin kudu maso gabas
  • Shahararrun kungiyoyi irinsu Ohanaeze Ndigbo, Nzuko Umunna, da Alaigbo Development Foundation sun daga muryoyinsu wajen kira ga shugabancin Ibo a 2023
  • Zuwa yanzu dai wasu daga cikin yan siyasar kudu sun fara bayyana aniyarsu na neman kujerar

FCT, Abuja - A makonni masu zuwa, ana sanya ran cewa manyan yan siyasar Ibo za su ayyana aniyarsu na neman babban kujera ta daya a kasar.

Legit.ng ta jero wasu manyan yan siyasar kudu maso gabas wadanda ake sanya ran za su fafata a wajen neman tikitin shugaban kasa a jam'iyyunsu mabanbanta.

Yan siyasar kudu maso gabas 5 da ake sa ran za su fafata a zaben shugaban kasa a 2023
Yan siyasar kudu maso gabas 5 da ake sa ran za su fafata a zaben shugaban kasa a 2023 Hoto: OUK Media
Asali: Facebook

1. Sanata Anyim Pius Anyim

Dan siyasar haifaffen Ebonyi ya kasance tsohon shugaban majalisar dattawa kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya. Tuni ya ayyana aniyarsa na neman takarar shugaban kasa a jam'iyyarsa ta Peoples Democratic Party.

Kara karanta wannan

Fitaccen dan jarida, Dele Momodu ya ayyana kudurin tsayawa takara a 2023 a PDP

Shine shahararren dan siyasar Ibo na farko da ya bayyana ra'ayinsa na neman kujerar kuma tuni ya fara ziyartan manyan yan Najeriya a fadin kasar domin sanar da su ra'ayinsa na son shugabanci.

2. Mista Kingsley Moghalu

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya ma ya ayyana aniyarsa na son takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Moghalu wanda ya fito daga jihar Anambra, ya dade da komawa jam'iyyar African Democratic Congress don ganin mafarkinsa ya zama gaskiya.

Shine dan takara guda a wajen manyan jam'iyyun siyasar kasar na PDP da APC wanda ya sanar da kudirinsa. Ana masa kallon dan siyasa mara karfi.

3. Sanata Orji Uzor Kalu

Kalu ya kasance tsohon gwamnan jihar Abia kuma bulaliyar majalisar dattawa a yanzu. Yana daga cikin yan siyasar kudu maso gabas da ke sahun gaba a yanzu.

Kara karanta wannan

2023: Na manta ban sanar da Buhari zan yi takarar shugaban kasa ba - Tsohon mataimakin gwamnan CBN

An tattaro cewa Kalu yana gyara kwanjinsa domin shiga tseren kujera ta daya a kasar. A makonnin karshen 2021, irin baki da Kalu ya dunga tarba a gidansa na Abuja ya nuna cewa a shirye yake ya gwada sa'arsa.

4. Owelle Rochas Anayo Okorocha

Okorocha ya kasance tsohon gwamnan jihar Imo kuma sanata mai wakiltan Imo ta yamma a yanzu. Okorocha ba bako bane wajen takarar kujerar shugabancin kasar.

Kafin ya zama gwamnan Imo, ya yi kokarin zama shugaban kasar Najeriya sau biyu amma bai yi nasara ba. Ana yi masa kallon dan siyasa mai karfi da baki a fadin kasar wanda ka iya taimaka masa wajen cimma burinsa.

5. Gwamna David Umahi

Gwamnan na jihar Ebonyi na daya daga cikin yan siyasar kudu maso gabas da ke son gadar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Umahi ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a watan Nuwamban 2020 wanda hakan ya haifar da rade-radi game da kudirinsa na son zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

Tuni dai gwamnan ya sanar da kudirinsa na shiga tseren kujerar ta daya a kasar.

2023: Na manta ban sanar da Buhari zan yi takarar shugaban kasa ba - Tsohon mataimakin gwamnan CBN

A gefe guda, mai burin zama shugaban kasa, Kingsley Moghalu, ya bayyana cewa ya manta bai sanar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari aniyarsa na takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba.

Daily Post da Punch sun rahoto cewa, Moghalu wanda ya kasance tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 12 ga watan Janairu, a shafinsa na Twitter.

Ya wallafa a shafin nasa:

“Na manta ban sanar da Shugaban kasa @Mbuhari cewa zan yi takarar shugaban kasa ba. Amma na sanar da yan Najeriya, wanda shima yana daya daga cikinsu, don haka babu matsala.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel