2023: Ƴan Najeriya na son PDP ta karɓi shugabancin ƙasa daga hannun APC, Wike
- Gwamna Wike na Jihar Rivers ya bayyana cewa za suyi duk mai yiwuwa don karbo mulkin kasa a 2023
- Wike ya bukaci haɗin kan ƴaƴan jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, don samun nasara a zaɓe mai zuwa
- Gwamnan ya bayyana haka yayin da ya kai ziyara ga takwaran sa na Jihar Bayelsa a gidan gwamnati da ke Yenagoa
Jihar Bayelsa - Nyesom Wike, gwamnan Jihar Rivers, ya yi iƙirarin cewa ƴan Najeriya na fatan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta karɓe mulkin kasa a shekarar 2023, NewsWireNGR ta ruwaito.
Gwamna Wike ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyarar girmamawa ga gwamnan Jihar Bayelsa, Senator Douye Diri, a gidan gwamnatin Bayelsa, a Yenagoa, ranar Litinin.
Babbar Magana: Jam'iyyar APC ta maida zazzaafan martani ga kalaman Tinubu na takarar shugaban ƙasa a 2023
A wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan a bangaren yaɗa labarai, Kelvin Ebiri ya fitar ya bayyana cewa gwamnan ya yi kira gare su da su haɗa kai da shugabannin jam'iyyar don yin aiki tare.
Ya ce:
"Nazo ne don sanar da shi cewa dole kowa a matsayin mu na ƴan PDP muyi aiki tare don gina jam'iyyar.
"Idan babu jam'iyya babu batun ɗan takarar shugaban ƙasa. Dole sai da jam'iyya. Don haka akwai bukatar kowa muyi aiki tare, mu haɗa kan jam'iyyar kafin ayi batun wanda zai tsaya takarar shugabancin ƙasa.
"Baza mu sake muyi asarar wannan damar ba yadda ƴan Najeriya ke kwaɗayin PDP ta karɓe ragama a 2023. Dole muyi aiki tare a matsayin jam'iyya. A matsayin mu na gwamnoni, dole muyi aiki tare. Da bamu yi aiki tare ba, ba za mu iya gudanar da gagarumin taron da muka gudanar da irin sa a karon farko a tarihin jam'iyyar."
Hadimin Buhari: Surutai da barazana ba zai sa Arewa ta mika wa kudu shugabancin kasa a 2023 ba
A wani labarin daban, tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari a bangaren harkokin Majalisar Wakilai, Abdulrahman Suleman Kawu Sumaila, ya ce arewa ba za ta bar wa kudu shugabancin kasa ba saboda tsoratarwa da surutai, Daily Trust ta ruwaito.
Ya yi wannan maganar ne yayin mayar da martani a kan wata magana da Ministan Kwadago, Chris Ngige ya yi inda ya ce duk wata jam’iyyar da ta tsayar da dan arewa za ta fadi zaben shugaban kasa.
Sumaila, wanda tsohon dan majalisar wakilai ne ya ce ya kamata Ngige da ire-irensa su rufe kawunansu a kasa saboda kunya a kan kokarin tsoratar da arewa wurin batun shugabancin kasa na shekarar 2023.
Asali: Legit.ng