2023: Katafaren fostan neman zaben shugaban kasa na Osinbajo ya karade titin Abuja

2023: Katafaren fostan neman zaben shugaban kasa na Osinbajo ya karade titin Abuja

  • Gabannin zaben shugaban kasa na 2023, fostan yakin neman zaben shugaban kasa na mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana a Abuja
  • An gano fostan ne manne a wata gadar sama da ke tsakiyar babbar birnin tarayyar kasar
  • Sai dai babu suna ko tambarin wata jam'iyya illa sunan kungiyar da ta dauki nauyinsa

Abuja - Wani katafaren fostan yakin neman zaben shugaban kasa dauke da suna da hoton mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana a Abuja, babbar birnin tarayyar kasar.

Osinbajo wanda ya kasance dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, yana wa’adinsa na biyu a matsayin mataimakin shugaban kasa tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

2023: Katafaren fostan neman zaben shugaban kasa na Osinbajo ya karade titin Abuja
2023: Katafaren fostan neman zaben shugaban kasa na Osinbajo ya karade titin Abuja Hoto: The Punch
Asali: UGC

Jaridar Punch ta rahoto cewa an manna fostan kamfen din ne a jikin wata gadar sama a tsakiyar birnin tarayyar kasar dauke da hoton Osinbajo.

Kara karanta wannan

Ba za ta yiwu a tsaida Musulmi da Musulmi takara ba, sama da kasa za su hade inji CAN

Fostan na dauke da rubutu kamar haka “Ku taya mu, Najeriya na bukatar Osinbajo a 2023.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Koda dai ba a rubuta suna ko tambarin jam’iyya a kan babban fostan ba, yana dauke da sunan wata kungiya ‘The Progressive Project 2023’ a matsayin wacce ta dauki nauyin sa.

Akwai rade-radin cewa Osinbajo na iya nuna ra’ayin takara a zaben shugaban kasa na 2023.

Jaridar ta kuma rahoto cewa tuni wasu kungiyoyi suka fara ayyana goyon bayansu a gare shi.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin babban jagoran APC na kasa, Bola Tinubu zai fito takarar shugaban kasa.

Dan majalisar Kano ya bayyana mutum daya rak da ya cancanci darewa kujerar Buhari a 2023

A gefe guda, gabannin zaben 2023, wani dan majalisar Kano mai wakiltan mazabar Tarauni a majalisar wakilai, Hafiz Kawu ya bayyana cewa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya cancanci darewa kujerar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

2023: Osinbajo ne ya dace ya gaji Buhari, Dan majalisar Kano, Hafizu Kawu

Kawu ya bayyana cewa Osinbajo ya cancanci ya gaji Buhari a matsayin shugaban kasa na gaba bisa ka'idojin shari'a, biyayyarsa da kuma ci gaba da aiwatar da ayyukan da gwamnatin ta fara da dai sauransu.

Dan majalisar ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano kan harkokin siyasa da ci gaban kasar, Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng