Ina goyon bayan Buhari kan kin sanya hannu a dokar zabe, Sanata Adamu
- Sanata Abdullahi Adamu ya yi martani a kan matakin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kin sanya hannu a dokar zabe
- Adamu ya bayyana cewa yana goyon bayan hakan dari bisa dari
- Ya ce rashin adalci ne a zo da wani doka da zai takaita yadda jam’iyyu za su gudanar da zabensu
Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana a ranar Laraba, 29 ga watan Disamba, cewa ya yi farin ciki da ganin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai sanya hannu a gyararren dokar zabe ba.
Adamu ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya a Keffi cewa Majalisar dokokin bata da hurumin aiwatar da wani kudiri da zai yanke yadda jami’iyyu za su zabi yan takararsu.
Adamu ya ce:
“Bakon abu ne kuma rashin adalci ne a zo da wani doka da zai takaita yadda jam’iyyu za su gudanar da zabensu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Ina goyon bayan shugaban kasa a kan kin saka hannu a kudirin.
“Ya kamata mu yi godiya cewa kin saka hannun da Buhari yayi yana da amfani sosai. Shi mutum ne mai alkibla; mai zurfin tunani da tsare-tsare.”
Adamu, wanda ya kasance shugaban majalisar dattawa kan noma, ya ce ya yarda da dalilan da Shugaban kasar ya bayar na kin sanya hannu a kudirin, rahoton Punch.
“Gwiwowin wasu mutane ya sace saboda ganin cewa zai yi wuya samun kaso biyu cikin uku na mambobi don dawowa zauren.
“Abun damuwa ne. Na damu da hakan sosai amma gyaran ba wai shine mu kafa dokoki domin wasu ra’ayi namu na kanmu ba.
“Jam’iyyun na da nasu tsare-tsaren da ka’idoji wanda mutane suka amince da su don zama mambobi.”
A cewarsa, ba za ka zama dan wata jam’iyya ba sannan idan ka kai wajen ka ce za ka canja tsarin wasan ba. Ba daidai bane; babu adalci.
Sai dai kuma, ya bayyana cewa yan majalisan za su yanke hukunci kan dokar idan suka dawo a watan Janairun 2022, ruwayar Pulse.ng.
Buhari: Sanatoci su na kokarin hada-kai domin gyara dokar zabe da karfi da yaji ta Majalisa
A gefe guda, mun ji cewa a ranar Talata, 21 ga watan Disamba, 2021, Sanatoci suka fara yunkurin warware matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka.
Daily Trust tace ‘yan majalisa su na so ayi wa dokar zabe garambawul bayan shugaban Najeriyar ya ki amincewa da kudirin da zai wajabta zaben ‘yar tinke.
‘Yan majalisar dattawan sun tado wannan magana ne yayin da suka yi zaman farko a makon nan. Da alamun za su daga hutunsu saboda wannan magana.
Asali: Legit.ng