2023: Babban faston Najeriya ya bayyana wanda zai gaji Buhari
- Yayin da kallo ya koma sama kan wanda zai gaji shugaba Muhammadu Buhari a 2023, babban fasto, Primate Ayodele ya saki hasashensa kan wanda zai dare kujerar
- Daga cikin wadanda ya ce za su iya darewa kujerar akwai Rabiu Kwankwaso, Babgana Zulum, Bukola Saraki, Abubakar Malami da sauransu
- Sai dai kuma bai ambaci Atiku Abubakar, Bola Tinubu da Yahaya Bello cikin wadanda ka iya yin nasara ba
Yayin da shekarar 2023 ke kara gabatowa, 'yan Najeriya da dama sun zuba ido domin ganin wanda zai karbi mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari gabannin babban zabe mai zuwa.
A cikin haka ne babban faston cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya saki hasashensa na abubuwan da za su faru a 2022.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, babban malamin na addinin Kirista, ya ambaci wasu manyan yan siyasa da ka iya zama shugaban kasar Najeriya da mataimakinsa a 2023.
Sai dai kuma a cikin sunayen da limamin cocin ya ambata babu sunayen wasu manyan yan siyasar kasar wadanda ake ganin suna cikin wadanda ke hararar kujerar Buhari da Osinbajo.
Daga cikin yan siyasar da ba a ambaci sunayensu ba akwai babban jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da kuma gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.
Idan za ku tuna yan Najeriya da dama suna ta kiraye-kiraye ga shugabannin uku a kan su shiga tseren kujerar shugaban kasa a 2023.
Sai dai kuma har yanzu babu wanda ya fito ya kaddamar da aniyarsa na neman kujerar a hukumance.
Sunayen yan takarar da faston ya ce za su iya zama shugaban kasa na gaba
Amma kuma, Primate Ayodele ya ambaci sunayen wasu gwamnoni da manyan kasar cikin wadanda ka iya darewa kujera ta daya a kasar.
Daga cikin wadanda ya ambata a bangaren jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP akwai; Aminu Waziri Tambuwal, Nyesome Wike, Bukola Saraki, Samuel Ortom da Bala Mohammed
Ya kuma ambaci Rabiu Musa Kwankwaso da Emmanuel Edom a matsayin wadanda ka iya yin nasara.
Har wa yau, Ayodele ya ambaci Abubakar Malami, Boss Mustapha, Kayode Fayemi, Rotimi Amaechi, Prof. Babagana Umara Zulum, Babatunde Fashola, Mai Mala Buni, Ibikunle Amusun, da Aregbesola Rauf a bangaren APC.
Primate Ayodele ya ce:
"Shigar Tinubu harkar shugabanci ba zai inganta Najeriya ba.
“Za a dakatar da shirin Yahaya Bello na zama shugaban kasa kuma jam’iyyarsa za ta kawo cikas ga yunkurinsa.
"Kada Doyin Okupe ya yi asarar kudinsa kan kowani zabe.
“Nyesom Wike zai yi gwagwarmayar neman babban matsayi a jam’iyyar PDP kuma zai yi burin zama na daya.
“Majalisar dattawa da gwamnoni za su fafata kan wanda zai zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC.
"Haka kuma, kada Sule Lamido ya yi asarar kudinsa kan zabe.
“Goodluck Jonathan will lose his past and present day glory. There will be pressure on
him.
“Goodluck Jonathan zai rasa daukakarsa ta baya da yanzu. Za a matsa mashi.
“Farfesa Yemi Osinbajo mutumin kirki ne amma zai sha badakala. Za kuma su haifar masa da makiya."
A kusan karon farko, rikakken ‘Dan adawa, Sule Lamido ya yabawa matakin da Buhari ya dauka
A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, yace zai fi dacewa a bar jam’iyyu su fitar da tsarin da suke sha’awa wajen tsaida ‘dan takara.
Jaridar Daily Trust ta rahoto Sule Lamido yana cewa bai dace a ce wasu a gefe ba ne za su zabawa jam’iyyun siyasa yadda za su fito a ‘dan takararsu a zabe.
Da yake magana da manema labarai a gidansa da ke Bamaina, garin Birnin Kudu a ranar Lahadi, 26 ga watan Disamba, 2021, Sule ya bada wannan shawara.
Asali: Legit.ng