Babbar magana: Kwamishiniya a Zamfara ta yi murabus domin ta samu mukami a jihar Imo
- Kwamishinaya a jihar Zamfara ta yake shawarar aje aikinta domin komawa jihar Imo ta samu mukamin kwamishina
- Rabi Shinkafi ta bayyana dalilin da yasa ta yanke wannan shawari, ta kuma ce babu wata matsala tsakaninta da gwamnatin Zamfara
- Hakazalika, ta mika godiya ga gwamnan jihar Zamfara da matarsa bisa karramata da ba ta damar aiki a jihar
Gusau, Zamfara - Kwamishiniyar harkokin mata da kananan yara ta jihar Zamfara, Rabi Shinkafi, ta yi murabus daga mukaminta domin sake daukar mukamin kwamishina a jihar Imo, PM News ta rahoto.
Yayin da take bayyana ficewarta daga mukamin a jihar Zamfara, Rabi ta kuma mika godiya ga gwamnan jihar, Bello Matawalle.
Shinkafi ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Gusau ranar Alhamis 23 ga watan Disamba cewa:
“Na ajiye mukamina na kwamishina a Zamfara ne domin in sake samun nadin a matsayin kwamishina a Imo.
“Ina matukar godiya ga Gwamna Bello Matawalle da uwargidansa Hajiya A’isha Matawalle bisa yadda suka nuna min karimci tare da ba ni dama na yi wa Zamfara hidima a ayyuka daban-daban.
Daily Nigerian ta tattaro cewa, yayin da take wanke duk wani zargi na matsala da sabani da gwamnatin jihar Zamfara, ta bayyana cewa:
“Duk zarge-zarge da ake ta yadawa a kafafen sada zumunta game da murabus dina duka karya ce; aiki ne kawai na masu yada barba.
“Ina da cikakkiyar dangantaka da gwamna da matarsa. Ina daukar su a matsayin dangina kuma suna goyon bayan tafiyata Imo.
"Dukkanins, Gwamna Hope Uzodinma na Imo da Matawalle sun tattauna a matsayin gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress kuma abokai."
Majalisar dokokin Imo ta tsige wasu ‘yan majalisa 3 saboda dalilai
A wani labarin, a ranar Alhamis ne majalisar dokokin jihar Imo ta tsigewasu ‘yan majalisar dokokin jihar guda uku, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Tsigewar ta faru ne a farfajiyar majalisar bayan sanarwar da kakakin majalisar, Kennedy Ibeh ya bayar.
‘Yan majalisar da aka tsigen sun hada da Arthur Egwim (Ideato ta Arewa) Ngozie Obiefule (Isu) da Obinna Okwara (Nkwerre).
Asali: Legit.ng