Kwankwaso yace Buhari ba zai saka hannu a ƙudirin zaɓe ba, ya bada dalili, ya faɗa abinda ƴan majalisa zasuyi
- Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya bayyana dalilin da yasa ya yi imanin Buhari ba zai saka hannu kan kudin gyaran dokar zabe ba
- Kwankwaso ya yi ikirarin cewa gwamnonin jihohi ne suka yi wa Shugaban kasa matsin lamba kada ya saka hannu kan kudirin dokar saboda batun zaben 'yar tinke
- Tsohon gwamnan ya ce duk da cewa zaben fidda gwani na 'yar tinke ya fi kyau, gwamnoni ba su son hakan domin zai rage musu karfin iko
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano, ya yi ikirarin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba zai saka hannu ba kan kudirin gyaran dokar zabe ba saboda gwamnoni sun bukaci kada ya amince don zaben 'yar tinke.
The Punch ta rahoto cewa Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin hirar da aka yi da shi gabanin zaman majalisar tarayya.
A cewar tsohon gwamnan na Kano, wajabta zaben 'yar tinke zai bada daman wanda ya fi farin jini ya lashe zabe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma, ya ce, gwamnonin ba za su goyi bayan hakan ba domin wajabta zaben 'yar tinken zai rage musu karfi.
Ya ce:
"A shekarar 1999, an zabe ni matsayin dan takarar PDP ta hanyar 'yar tinke amma daga bisani muka gano akwai matsala tattare da 'yar tinke.
"Yana da wahalar yi saboda yawan mutane; akwai nakasu nan da can amma bayan amfani da tsarin wakilai, zan iya cewa 'yar tinke ta fi tsarin wakilai."
Kwankwaso ya ce gwamnonin da wasu 'mutane masu karfi' ba za su taba son a amince da 'yar tinke ba domin iko zai fice daga gidajen gwamnati ya koma hannun masu zabe da mambobin jam'iyyar.
Ya kara da cewa yana da wahala Shugaba Buhari ya saka hannu kan kudirin dokar zaben.
Da aka tambaye shi idan yana da tabbas Buhari ba zai saka hannu a dokar ba, Kwankwaso ya jadada cewa Buhari ba zai saka hannu kan zaben ba tunda APC ta tabbatar Majalisar Tarayya bata saka hannu kan dokar ba a watan da ya gabata.
Majalisar Tarayya ba za ta yi amfani da karfin ikonta ba wurin amincewa da dokar - Kwankwaso
Ya kuma ce Majalisar Tarayya ba za ta yi amfani da karfin ikon ta ba domin amincewa da dokar idan Shugaba Buhari bai saka hannu kan dokar ba.
A cewarsa, Majalisar Tarayya na yanzu ta nuna cewa ita wani sashi ne kawai na bangaren masu zartarwa.
Ya ce tunda Shugaban Majalisa ya ce dukkan bukatun Buhari alheri ne ga Najeriya, hakan na nufin cewa ba za su iya juya wa matakin shugaban kasar ba.
Martanin 'yan Najeriya
Timiebi Moses Tamara-Ekpezu a Facebook ya ce:
"Ya fi sauki ga majalisa su yi dokar da za su hallata ciyo bashi mai yawa, yan bindiga, garkuwa da mutane, kisa da makiyaya da yan ta'adda a kasar nan a maimakon shugaban kasa yasa hannu kan kudirin dokar zabe."
Martins Martins Egiri ya ce:
"Buhari ya taimake mu da wannan, kafin ya kyalle mu ya koma gonarsa, wannan kasar ta sha wahala don haka ya taimake mu, rokonsa muke yi."
Ekpezu Nse Daniel ya ce:
"Tunda farko, na san cewa ba zai saka hannu kan kudirin ba. Ta yaya za su cigaba da mulki idan ya saka hannu kan kudirin."
Martins Amadi ya ce:
"Ba bukatar a yi zabe da wannan tsarin zaben mai matsala na yanzu. Idan yan Najeriya ba su da tabbas cewa kuri'arsu za ta yi tasiri, kawai mu nuna wanda muke so ya hau ..."
Buhari: Da zarar na kammala wa'adin mulki na zan koma gona ta a Daura in tare
A wani labarin, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya na da kudirin komawa gonarsa ta Daura, mahaifarsa da ke jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kasa ya furta hakan ne a Istanbul, kasar Turkiyya inda aka shirya masa bikin zagayowar ranar haihuwarsa ba tare da saninsa ba a ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar.
Buhari ya na kasar Turkiyya yanzu hakan don halartar wani taro inda har ranar haihuwarsa ta zagayo, ya cika shekaru 79 kenan a ranar Juma’a.
Asali: Legit.ng