Da Dumi-Dumi: Gwamnan Jam'iyyar APC ya naɗa sabbin kwamishinoni 15

Da Dumi-Dumi: Gwamnan Jam'iyyar APC ya naɗa sabbin kwamishinoni 15

  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya aike da sunayen sabbin kwamishinoni 15 zuwa majalisar dokokin jihar
  • Tun a watan Agusta, 2021, gwamnan ya sallami baki ɗaya hadimansa, ya bar kaɗan daga cikin kwamishinoni
  • Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta baiwa mutanen wa'adin daga nan zuwa Talata su mika kwafin CV domin fara aikin tantancewa

Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya naɗa sabbin kwamishinoni 15 a jiharsa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Wannan na kunshe ne a wata wasika da gwamnan ya rubuta wa majalisar dokokin jihar kuma aka karanta a zaman majalisa na yau Alhamis.

Yayin da yake karanta wasikar a zauren majalisar dokokin, shugaban masu rinjaye, Honorabul Umar Tanko-Tunga, yace gwamnan ya roki mambobin majalisa su maida hankali yadda ya dace kan naɗin.

Kara karanta wannan

Kano: Ilimin Addinin Musulunci Ka Ke Buƙata Ba Boko Ba, Tsohon Kwamishina Ya Faɗa Wa Ganduje

Gwamnan Nasarawa
Da Dumi-Dumi: Gwamnan Jam'iyyar APC ya naɗa sabbin kwamishinoni 15 Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Su waye gwamnan ya naɗa?

Waɗan da gwamnan ya amince da naɗinsu, sun haɗa da; Yakubu Kwanta (Akwanga), Yusuf Aliyu Turaki (Awe), da Aisha Rufai-Ibrahim (Awe).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai kuma Salihu Ena (Doma), Umar Mukailu Gurku (Karu), Nuhu Oshafu (Keana) da kuma Idris Mohammed Idris (Keffi).

Sauran sun haɗa da; Abdulkarim Kana (Kokona), Mohammed Sarki- Tanimu (Lafia), Abimiku Hanatu-Bala (Lafia), Fati Jimeta-Sabo (Nasarawa), Mohammed Yakubu-Lawal (Nasarawa Eggon) da kuma Daniel Agye (Obi).

Sai kuma ragowar mutum biyu, Pharm. Ahmed Baba-Yahaya daga ƙaramar hukumar Toto da kuma Ambasada Lucky Isaac daga ƙaramar hukumar Wamba.

Majalisa ta saka wa'adi

Majalisar ta saka wa'adin ranar Talata ga waɗan da gwamnan ya tura sunayensu, su mika mata kwafin bayanan karatunsu (CV) domin fara aikin tantancewa.

Legit.ng Hausa ta gano cewa tun a ranar 30 ga watan Agusta, 2021, gwamnan ya sanar da rushe yan majalisarsa, inda ya bar kwamishinoni kaɗan.

Kara karanta wannan

Shugaban ICPC ya tono kwangilolin da aka ba Sanatan APC, ya kai wa Buhari hujjoji

A wani labarin na daban kuma Jam'iyyar APC ta ƙasa ta bayyana matakin da zata dauka kan Ganduje da Shekarau bayan hukuncin Kotu

Jam'iyyar APC tace har yanzun tana dakon kwafi na asali na hukuncin da kotu ta yanke kan zaɓen shugabanni a Kano.

Sakataren APC na kasa, Sanata James, yace jam'iyya zatai nazari kan hukuncin kafin ta ɗauki matakin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel