Rikicin APC a Zamfara: Tsagin tsohon gwamna Yari ya caccaki Yeriman Bakura, yace munafuncinsa ba zai nasara ba

Rikicin APC a Zamfara: Tsagin tsohon gwamna Yari ya caccaki Yeriman Bakura, yace munafuncinsa ba zai nasara ba

  • Tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yerima, ya shiga cikin waɗan da ake zargi da rura wutar rikicin APC a jihar
  • Ana zargin Yerima da maganganun wuce gona da iri kan ƙarar da wasu mambobin APC suka shigar a gaban kotu
  • Tsagin APC dake nuna goyon baya ga Abdul'azizi Yari, yace Yerima ya fusata ne saboda gaza cimma burinsa na takarar shugaban ƙasa

Zamfara - Tsagin jam'iyyar APC dake goyon bayan tsohon gwamna, Abdul'aziz Yari, ya caccaki Sanata Ahmed Sani Yerima, bisa furucinsa game da karar dake gaban kotu.

Kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa bisa jagorancin gwamna Mala Buni na Yobe, ya sanar da rushe kwamitin gudanarwan APC a Zamfara biyo bayan sauya shekar gwamna Matawalle a watan Yuni.

Kara karanta wannan

Ba dalilin da zai sa APC ta sha ƙasa a zaben 2023 domin yan Najeriya na jin dadin mulkin Buhari, Gwamna

Legit.ng ta gano cewa Saboda rashin gamsuwa da matakin, ɓangaren Yari suka garzaya gaban kotu suna kalubalantar matakin kwamitin na rushe shugabannin APC.

Ahmed Sani Yerima
Rikicin APC a Zamfara: Tsagin tsohon gwamna Yari ya caccaki Yeriman Bakura, yace munafuncinsa ba zai nasara ba Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Me Sanata Yerima ya faɗa kan lamarin?

Da yake tsokaci kan lamarin a wani taro da ya gudana a ƙarshen mako, Yerima yace bada jimawa ba kotu zatayi watsi da karar dake ƙalubalantar rushe shugabannin APC.

Yace kotu ba zata amince da kowane ɓangaren jam'iyyar APC ba a jihar, inda yace:

"Tunda uwar jam'iyya ta ƙasa na tare da gwamna, to ba abinda kotu zata iya yi kan lamarin."

Hakan baiwa yan tsagin Yari daɗi ba

Da suke martani kan wannan furucin, tsagin Yari ta bakin shugabansu, Alhaji Lawal Liman, sun yi watsa da kalaman Yerima.

Liman yace:

"Abun takaici ne Yerima ya maida hankali wajen abubuwan da zasu kara kirkiro matsaloli ga mutanen Zamfara. Bai taba magana kan matsalar tsaro ba, a lokacin da mahaifarsa karamar hukumar Bakura ke kan gaba."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta bayyana matakin da zata ɗauka kan Ganduje da Shekarau bayan hukuncin Kotu

"Bai taba ganin ya dace ya gabatar da kudiri kan matsalar ba a majalisar dattijai tsawon shekara 12 yana wakilatar mutane. Makon da ya gabata mahara suka rufe hanyar Kauran Namoda-Shinkafi, an kashe mutane da dama da asarar dukiya."
"Kamar haka ta faru a yankunan kananan hukumomin Maru, Bungudu da Tsafe. Ba zaka taba jin Yerima ya jajantawa mutane ba, a koda yaushe ya fi maida hankali wajen rura wutar rikici tsakanin mambobin jam'iyya."

Yaushe Yerima ya zama alkali?

A cewar Liman saboda gaza kai bantensa a kokarinsa na zama shugaban ƙasa yasa Yerima faɗa da kowa a siyasance.

"A wani bidiyo da muka gani, mun ji Yerima na baiwa gwamna shawara ya rushe dukiyar yan siyasan dake adawa da shi. Ya koma yana faɗa da zargin kowa saboda gaza cimma kudirinsa na shugabancin ƙasa."
"Ba mu san lokacin da Yerima ya zama Alkali ba, mun san dai ba'a siyan kotu ko a mata barazana."

Kara karanta wannan

Malamin Jami'a a arewa ya rasa aikinsa saboda lalata da ɗalibansa mata

A wani labarin kuma wani Jiga-Jigan Jam'iyyar APC da dandazon mambobi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a Kalaba

Cross River - Tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke, tare da manyan jiga-jigan PDP sun karbi tawagar masu sauya sheka daga APC.

A cewar ɗaya daga cikin tsaffin yan APC ɗin, komawarsu PDP tamakar komawa gida ne domin daman nan ne asalin su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262