Zaben 2023: Shugaba Buhari ya rubuta wasika zuwa ga Hukumar Zabe INEC
- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya rubuta wasika zuwa ga hukumar zaɓe INEC, ya nemi shawara kan dokar zabe 2021
- Buhari ya nemi hukumar ta yi tsokaci kan sabon kudirin dokar zaɓe da majalisa ta tura masa kan zaben fidda gwani kai tsaye
- A halin yanzun ana jiran shugaban ya rattaba hannu kan dokar, wacce zata baiwa yan Najeriya damar fidda ɗan takara da kan su
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya rubuta wasika zuwa ga hukumar zaɓe INEC, yana neman shawararta kan kudirin sabbin dokokin zabe 2021.
Wasikar mai dauke da adireshin shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, Buhari ya nemi jin ta bakin hukumar kan kudirin dokar zaɓen fidda gwani na jam'iyyu kai tsaye.
Dailytrust tace Buhari ya nemi shawarar INEC kan zartar da dokar zaɓen fidda gwani kai tsaye ga jam'iyyun siyasa yayin fidda ɗan takara da sauran muhimman batutuwa.
Yadda kudirin ya jawo cece-kuce
Wasu daga cikin gwamnoni da yan majalisu sun nuna kin amincewarsu da garabawul ɗin dokokin zaɓen, saboda saka zaben fidda gwani kai tsaye.
A ranar 9 ga watan Nuwamba, 2021, yan majalisun tarayya suka amince da dokar wacce zata baiwa mutane damar fitar da ɗan takarar jam'iyya.
A watan da ya gabata, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, yace abinda mambobin majalisarsa ke tsammanin shine shugaba Buhari zai rattaba hannu kan dokokin zaɓe 2021 su zama doka.
Haka nan kuma, kakakin majalisar dokokin tarayya, Femi Gbajabiamila, yace shugaban kasa Buhari na goyon bayan dokar zaben fidda gwani kai tsaye.
Sanatoci da yan majalisar wakilai zasu iya dawo da kudirin su zartar da shi idan shugaban ƙasa ya ƙi sa hannu bayan kwana 30.
Kudirin zai zama doka idan kowace majalisa ta samu kashi 2 cikin uku na mambobinta suka amince da shi kamar yadda aka tura wa shugaban ƙasa.
Shugaba Buhari zai nemi shawara
Babban hadimin Buhari ta bangaren yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, ya shaida wa Punch cewa Buhari zai cigaba da neman shawaran masu ruwa da tsaki kafin ya rattaba hannu.
Shehu yace:
"Shugaban ƙasa zai nemi shawaran waɗan da ya san cewa suna da ta cewa, da kuma waɗan da zasu iya ba shi shawara kan kudirin, sannan zai gana da su."
"Amma ba zan iya bayyana sunaye ko ayyana waɗan da shugaban zai nemi gana wa da su ba, shike da ikon yanke wa da kansa."
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta dare gida biyu, Matasa sun tsige Mala Buni sun nada sabon shugaba
Rikicin jam'iyyar APC ta ƙasa ya bude sabon shafi, yayin da matasan jam'iyyar suka sanar da rushe kwamitin rikon kwarya na Mala Buni.
Matasan karkashin kungiyarsu PYM, sun kuma rantsar da sabbin shugabanni da mambobin sabon kwamitin rikon kwarya da suka naɗa.
Asali: Legit.ng