Najeriya ba za ta iya juran azabtarwar APC na karin shekaru hudu ba, inji PDP
- Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Aminu Tambuwal ya bayyana cewa Najeriya ba za ta iya jure wasu shekaru hudu a karkashin jam’iyyar ba
- Tambuwal ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza ta kowani bangare a kasar
- Gwamnan na jihar Sokoto, ya kuma bayyana cewa ya zama dole kasar ta rungumi sake fasalin lamura domin tsira
Gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun ce Najeriya ba za ta iya jure wasu shekaru hudu a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba, rahoton Daily Trust.
Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya bayyana hakan a ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba a wajen bude wani taron jam’iyyar na kwana biyu.
Taken taron shine “Lokaci yayi da za a ceto da kuma sake gina Najeriya.”
A ruwayar Vanguard, Tambuwal ya kuma ce ya zama dole Najeriya ta rungumi garambawul domin tsira.
Tambuwal ya ce:
“Ya zama dole ta sauya fasalin siyasa, tattalin arziki, tsaro da kuma yadda take gudanar da abubuwa. Dole ta rungumi cin gashin kanta da canja tsarin mulki. Wannan zai karfafa gwiwar mutanenmu, musamman matasa. Lokaci yayi da ya kamata a bari Najeriya ta bunkasa. Za a cimma haka idan aka hada hannu.
“Shin Najeriya za ta iya jure wasu shekaru hudu na mulkin APC? Ansar ita ce a’a. PDP ce kadai madadin APC kuma ba za mu iya gazawa yan Najeriya ba. Ya zama dole mu tabbatar da ganin mafarkinsu ya zama gaskiya. Za mu iya aikata hakan. Eh, za mu iya, kamar yadda Obama yake fadi.”
Tambuwal ya ce ya zama dole PDP ta shirya dabarar kwace mulki a 2023 kamar yadda gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza kai kasar zuwa ga matakin da yan Najeriya ke tsammani a shekaru shida da suka gabata.
Ya ce:
“Mota mara birki ba za ta iya kai Najeriya inda take mafarkin zuwa ba. A yanzu PDP ce mota mai sabis da za ta iya kai Najeriya inda muke mafarkin zuwa.
“Shakka babu lokaci yayi da za a ceto da kuma sake gina Najeriya. Najeriya na bukatar aiki cikin gaggawa. Najeriya na cikin wani yanayi na bukatar taimakon gaggawa.
"Dukkanmu mun san menene matsalolin. Mutane ne suka haddasa su don haka ana iya magance su. Tana bukatar mayar da hankali, jajircewa, hikima da zukata masu dattako domin kai ta gaba. Eh tana bukatar shugabanci, hangen nesa da ladabtarwa.
“Mun yi fama da rikicin shugabanci. Hadin kan Najeriya na fuskantar matsaloli. Rayuwa a Najeriya ya zama mai wahala da gajarta yayinda rashin tsaro ya dabaibaye kasar.”
Ya ce APC mai mulki ta nuna gazawa wajen kula da albarkatun kasar inda yace:
“Tsakanin kaso 35 zuwa 40 na yan Najeriya basu da aikin yi kuma abun ya fi shafar mata da matasa.
“‘Yan bindiga, masu garkuwa da mutane, yan ta’adda duk suna cin karensu ba babbaka. ‘Ya’yanmu basu tsira ba a makarantunsu. Har yanzu akwai rashawa sosai a kasar.”
Tambuwal ya bayyana wanda ‘Yan Najeriya suke bukata ya zama Shugaban kasa a 2023
A gefe guda, mai girma gwamnan jihar Sokoto, ya yi kira ga jama’a da su guji zaben wanda zai rika daukar wasu bangare na kasar nan kamar ribatattun yaki.
Jaridar The Cable tace Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taron shari’a da aka shirya a babban birnin tarayya Abuja.
Mai girma Aminu Waziri Tambuwal yace idan an zo zaben 2023, ya kamata mutane su zabi shugaban da zai iya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Asali: Legit.ng