Har bayan wata 7, an kasa sasanta rikicin Kwankwaso da Wali a PDP
Idan za a tuna, zaen shugabannin jam'iyya na yankin arewa maso yamma an dakatar da shi bayan rikicin da bangaren tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da na tsohon ministan al'amuran waje, Ambasada Aminu Wali suka fara kan mukamin mataimakin shugaban jam'iyya.
Daily Trust ta wallafa cewa, mukamin wanda aka ayyana dan jihar Kano ne zai samu, ya tada kura tsakanin bangarorin biyu masu fatan cafke mukamin domin kara musu haske a shekarar 2023.
Mukaman 17 na yankuna sun hada da manyan mukamai 7 wadanda za a rarrabe tsakanin jihohi 7 na arewa. Jihohin sun hada da Jigawa, Kaduna, Katsina, Kano, Kebbi, Sokoto da Zamfara.
A yayin taron a kasuwar duniyar a ranar 10 ga watan Afrilu, magoya bayan Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da na Kwankwaso, lamarin da ya kawo dalilin dage zaben.
Kwankwaso ya zargi Tambuwal da hada kai da Wali wurin karantsaye a cikin lamurran jam'iyyar a Kano, zargin da gwamnan jihar Sokoton ya musanta.
Wannan halin da aka shiga ya tirsasa jam'iyyar kafa kwamitin kula na yankin, Daily Trust ta wallafa.
Amma rikici tsakanin Kwankwaso da Wali an fara shi tun 2018 yayin da tsohon gwamnan ya koma PDP kuma shugabancin jam'iyyar na kasa ta bashi kashi 51 na karfin ikon juya jam'iyyar.
Hakan ya bar sauran jihar da karfin ikon juya kashi 49 wanda za a raba tsakanin tsohon gwamna Ibrahim Shekarau, Wali da Sanata Bello Hayatu Gwarzo.
Mai magana da yawun Kwankwasiyya kuma jigon PDP a jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya sanar da Daily Trust cewa bayan lamarin da ya faru a Kaduna, Kwankwaso ya so a sasanta tsakaninsa da Tambuwal da Wali.
Ya zargi Tambuwal da hada kai da Wali wurin daukar nauyin Sanata Bello Hayatu Gwarzo domin neman mukamin.
Ya ce kungiyar Kwankwasiyya ba za ta kalmashe hannu ba ta zuba ido tana kallo dayar kungiyar na tozarta su ba.
Sai dai Muhammina Bako Lamido, shugaban bangaren Wali, ya jaddada cewa babu wata yarjejeniya kan tsayayyen dan takara kafin zaben.
"Mu ne 'yan asalin jam'iyyar tun a 1999. Ba mu taba barin jam'iyyar zuwa wata ba. Rabiu Musa Kwankwaso da magoya bayansa a wani lokaci a 2014 yayin da ya ke gwamna, ya yanke shawarar barin jam'iyyar zuwa APC amma muka tsaya a jam'iyyar mu,wannan ne tushen matsala.
"Kwankwaso ya ga kamar mun ci amanarsa saboda mun sanar da shi cewa ba mu son komawa jam'iyyar APC. A lokacin da ya yanke shawarar komawa PDP, ya ce mu ne makiyansa na farko kuma ba zai hada kai da mu ba wurin cigaban jam'iyyar saboda a wancan lokacin mun ki umarninsa," Lamido yace hakan ne tushen rikicin bangaren Wali da Kwankwaso.
Ya ce a lokacin da suka je Kaduna a watan Afirilu, sun je kada wa Sanata Beloo Hayatu Gwarzo kuri'a wanda shi ne uban jam'iyyar kuma tsohon sanata wanda ke neman mukamin.
Asali: Legit.ng