Kotu ta jefa Lauya Kurkuku kan zagin Kwamishanan lamarin addinai kan lamarin AbdulJabbar

Kotu ta jefa Lauya Kurkuku kan zagin Kwamishanan lamarin addinai kan lamarin AbdulJabbar

  • Sabuwar takkadama tsakanin Limanin Masallacin Juma'a, Kwamishanan addinai da wani lauya a jihar Kano
  • Kotu ta bada umurnin jefa lauyan gidan gyara hali kai zargin kokarin batawa Kwamishana Tahir Adam suna
  • An dage zaman kotun zuwa karshen wata kuma lauyan zai cigaba da zama a Kurkuku

Kotun Majistare dake Gidan Murtala a jihar Kano ranar Talata ta jefa wani Lauya, Hashim Hussei Hashim gida gyaran hali bisa zargin laifin zagin Kwamishana lamarin addinai, Tahir Adam.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa baya Lauyan ya saki bayanan rediyon inda ya caccaki Gwamnatin jihar Kano kan gurfanar da Malam Abduljabbar Kabara, kabara a kotu.

Lauyan yace sam Abduljabbar Kabara bai yi maganar batanci ga annabi ba.

Sakamakon haka, babban Limanin Masallacin Kwantin Kwari, Albakari Mika’il, ya kai Lauyan kara kotu kan yada labarin karya kansa da na kwamishanan.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda aka kusa halaka zababben gwamnan Anambra saura wata 8 zabe

A bidiyon jawabin, Lauyan ya ce Kwamishanan mugun mutum ne kuma shaidanin boye da kuma wasu kalaman batanci.

Amma yayin da ya gurfana a kotu, ya musanta haka kuma abokan aikinsa lauyoyi suka yi rokon a basa beli da sharadin ba zai sake irin wadannan kalamai ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotu ta jefa Lauya Kurkuku kan zagin Kwamishanan lamarin addinai kan lamarin AndulJabbar
Kotu ta jefa Lauya Kurkuku kan zagin Kwamishanan lamarin addinai kan lamarin AndulJabbar Hoto; Daily NIgerian
Asali: Facebook

Ya saba sharrudan beli

Amma bayan ba shi beli, lauyan ya sake sakin wani bidiyon inda yake alfahari babu wanda ya isa ya taba shi.

Shi yasa da aka koma kotu ranar Talata, Lauyan Kwamishanan, Lamido Sorondinki, ya bukaci kotu ta janye belin saboda Mr Hashim ya saba sharadin da aka sanya masa.

Alkali kotun, Hauwa Minjibir, tace a jefashi kurkuku zuwa karshen Nuwamba.

Lauyan yace:

"Da farko ya ce ayi hakuri. Yayi nadama cewa ba zai sake ba. Hakan na nufin cewa ya amsa laifinsa. Sai kotu ta jefashi gidan gyara hali zuwa 30 ga Nuwamba don cigaba da sauraran kara."

Asali: Legit.ng

Online view pixel