Anambra 2021: Jiga-jigan al'amura 10 da ya dace a sani game da zaben gwamna

Anambra 2021: Jiga-jigan al'amura 10 da ya dace a sani game da zaben gwamna

A yau, jama'ar jihar Anambra za su bayyana a akwatunan zabensu domin zaben gwamnan da zai mulki jihar nan gaba. Zaben ranar 6 ga watan Nuwamba shi ne na farko da za a yi na jihar a Najeriya wanda hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta shirya a 2021.

A cikin watannin da suka gabata, tsaro a jihar ya lalace, lamarin da ya dinga zama kalubale tare da tunanin yadda zaben zai kasance a yankin da kasar baki daya.

Jam'iyyun siyasa sun bayyana cewa, gangamin yakin neman zabensu ya samu tawaya sakamakon tsoron farmakin 'yan awaren IPOB.

Anambra 2021: Jiga-jigan al'amura 10 da ya dace a sani game da zaben gwamna
Anambra 2021: Jiga-jigan al'amura 10 da ya dace a sani game da zaben gwamna. Hoto daga Premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ga wasu muhimman abubuwa 10 da ya dace a sani game da zaben:

1. Sabbin akwatunan zabe

Kamar yadda INEC ta bayyana, an kirkiro akwatunan zabe 1,112 daga cikin wadanda akwai a jihar. Hakan zai sa jama'a su kara samun damar kada kuri'unsu ba kamar a baya ba da ake buga layikan zabe.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Bayani a kan ‘Dan takarar APC wanda ya taba yin Gwamna na kwana 17

2. Raguwar yawan masu kada kuri'a

Tun bayan dawowar damokaradiyya a 1999, zaben gwamnoni a Anambra bai taba fuskantar raguwar masu kada kuri'a da kashi 50 ba sai a 2007 inda aka tafka magudi kamar yadda CDD ta bayyana.

3. An aike jami'an tsaro masu yawa

A makon da ya gabata, Sifeta janar na 'yan sanda, Usman Alkali Baba, ya aike DIG biyu da AIG biyar zuwa Anambra domin taimako wurin tabbatar da tsaro a zaben Asabar.

4. Mutum 2.5 miliyan suka yi rijista

A farkon watan Oktoba, INEC ta ce ta yi wa mutum 2,525,471 rijista a jihar Anambra.

Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, ya ce hukumar ta samu wannan jimillar ne bayan cire 62,698 daga 138,802 da suka yi rijista a wata ukun farko na shekarar nan.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ƙungiyar IPOB ta saduda, ta soke dokar zaman gida na dole, ta ce a fita a yi zaɓe a Anambra

5. Kai kayayyakin aikin zabe wuraren ruwa

A shekarun bayan, INEC ta dinga fuskantar kalubale wurin kai kayayyakin zabe inda akwai rafi da tafkuna a jihar Anambra.

A rahoton kafin zabe, YIAGA ta yi kira ga INEC da jami'an tsaro da su kiyaye wuraren ruwa ruwa domin gudun taba nagartar zaben.

6. Kalubalen tsaro ga masu zabe, masu lura da zabe, malaman zabe da kayayyaki

Kamar yadda ake tsammani, zaben Anambra na cike da abubuwa daban-daban. 'Yan bindiga da 'yan awaren IPOB za su iya zama kalubale a zaben kamar yadda CDD ta sanar.

7. Amfani da sabuwar fasaha

INEC ta kawo sabon tsarin Bimodal Voter Accreditation System (BVAS), wani makwafin Smart Card Reader. Wannan tsarin ya na duba zanen hannu da fuska.

8. Jam'iyyun siyasa da 'yan takara

Akwai jam'iyyun 18 na siyasa da suke da 'yan takara a zaben gwamnan jihar Anambra na 6 ga Nuwamba kamar yadda INEC ta sanar.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya yi basaja ya kai ziyaran bazata asibiti, ya damke ma'aikata na karban kudin Haram

Rijistar karshe da aka gabatar, an bayyana jam'iyyun siyasa 18 da ke da 'yan takara, kwamishinan yace a watan Oktoba.

9. Rikicin cikin gida na jam'iyya

Babu shakka, kusan dukkan manyan jam'iyyun siyasa na Anambra cike suke da rikicin cikin gida. Jam'iyyun APGA mai mulki, PDP da na APC.

10. Shirin INEC

Baya ga samar da sabbin akwatunan zabe tare da sabon tsarin fasaha, INEC ta farfado daga hare-haren da aka kai wa hukumar inda ta zage tare da shirya zaben.

Zaben Anambra 2021: Dalilai 4 da za su iya sa Charles Soludo ya lashe zabe

A wani labari na daban, duk da akwai 'yan takara 18 tare da jerin jam'iyyun siyasa da suka fito gaba-gadi domin neman kujerar gwamnan jihar Anambra a zaben da za a yi ranar 6 ga watan Nuwamba, akwai 'yan takarar da babu shakka za a fafata da su.

Daga cikin 'yan takarar akwai Fafesa Charles Chukwuma Soludo, wanda shi ne dan takarar jam'iyya mai mulki a jihar ta All Progressives Grand Alliance (APGA).

Kara karanta wannan

A dage zaben gwamnan Anambra domin kare rayuka – Babban fasto ga FG

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng