Gwamnonin PDP hudu sun dira jihar Ondo da nufin zawarcin tsohon gwamnan jihar
- Gwamnonin jam'iyyar PDP hudu sun dira jihar Oyo da nufin zawarcin Olusegun Mimiko, tsohon gwamnan jihar ta Oyo
- Mimiko ya kasance dan jam'iyyar ZLP, wacce ya tsaya takarar sanata a karkashinta a zaben 2019
- Wasu jiga-jigan PDP a makon nan sun yi ishara da shigowar Mimiko zuwa jam'iyyar ta PDP, wanda yau gwamnonin jam'iyyar suka gana dashi
Oyo - Gwamnonin jam'iyyar PDP hudu sun isa jihar Ondo domin ganin tsohon gwamnan jihar, Olusegun Mimiko ya dawo jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.
Dimbin ‘ya’yan jam’iyyar ZLP sun hallara a gidan Mimiko da ke garin Ondo domin tarbar tawagar jam’iyyar PDP karkashin jagorancin gwamnan Oyo, Seyi Makinde.
Sauran Gwamnonin da ke cikin tawagar akwai Nyesom Wike na jihar Ribas; Okezie Ikpeazu na jihar Abia and Aminu Tambuwal na jihar Sokoto.
A halin da ake ciki suna ganawar sirri da Mimiko.
An tattaro cewa Gwamnonin za su tsara tattaunawa da Mimiko kan komawar sa jam’iyyar PDP
Majiyoyi sun ce ana sa ran Mimiko zai gana da shugabannin ZLP na jihar domin sanar da su komawarsa zuwa PDP a hukumance.
Ana sa ran tsohon mataimakin gwamna kuma dan takarar jam’iyyar ZLP a zaben gwamna na baya, Agboola Ajayi, zai koma jam’iyyar PDP tare da shi.
Mimiko a baya ya kasance mamba a jam’iyyar AD a shekarar 1999 kuma ya rike mukamin kwamishinan lafiya a gwamnatin marigayi Adefarati.
Ya koma PDP kuma, inda ya zama Minista a zamanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Sai dai an zabe shi Gwamna a jam’iyyar LP wanda daga baya ya koma PDP kafin karshen wa'adin mulkinsa.
Mimiko wanda aka fi sani da Iroko ya koma jam’iyyar ZLP gabanin babban zaben shekarar 2019 inda ya tsaya takarar Sanatan Ondo ta tsakiya amma ya sha kaye a hannun takwaransa.
A kwanakin nan, tsohon shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya yi ishara da shigowar wani gwamna zuwa jam'iyyar ta PDP, inda ya kara da cewa akwai wasu da ake sa ran za su shigo nan ba da dadewa.
Ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise.
Hakazalika, gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, shi ma ya yi batu makamancin wannan yayin hira da gidan talabijin na Channels a ranar 26 ga watan Oktoba.
2023: Najeriya za ta daidaita idan 'yan Najeriya suka ba PDP dama, inji gwamna
A wani labarin, Gwamnan jihar Akwa Ibom, Mista Udom Emmanuel ya ce akwai fatan alheri ga ‘yan Najeriya idan aka yi la’akari da gagarumin nasarorin da jam’iyyar PDP ta samu a matsayin jam’iyya a kasar.
Gwamnan ya yi wannan tsokaci ne a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, a Uyo, yayin da yake kaddamar da rajistar ranar gizo na mambobin jam’iyyar PDP reshen jihar Akwa Ibom.
Ya yi nuni da cewa irin kukan da ‘yan Nijeriya ke yi a halin yanzu saboda rashin shugabanci nagari, za a iya magance shi ta hanyar shugabanni masu kishin jama’a da jam’iyya irin ta PDP ke da su.
Asali: Legit.ng