Babban taro: Jerin sunayen ‘yan takara 27 da PDP ta tantance domin zaben kwamitin gudanarwa na kasa

Babban taro: Jerin sunayen ‘yan takara 27 da PDP ta tantance domin zaben kwamitin gudanarwa na kasa

  • PDP ta tantance tsohon shugaban majalisar dattawa, Iyorchia Ayu, tsohon gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola don takarar zaben kwamitin NWC
  • Hakazalika jam’iyyar adawar ta tantance tsohuwar ministar harkokin mata, Maryam Ciroma, tsohon gwamnan Oyo, Taofeek Arapaja da wasu sanatoci biyu
  • Gaba daya dai jimlar mutane 27 PDP ta tantance domin neman mukaman shugabancin jam’iyyar gabannin babban taronta

Abuja - Gabannin babban taronta na kasa wanda za a gudanar a ranar 30 ga watan Oktoba, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta tantance wasu mutane 27 domin yin takara a zaben kwamitin gudanarwa na kasa na jam'iyyar, Premium Times ta rahoto.

A ranar Laraba ne kwamitin shiyya na jam’iyyar ta tantance ‘yan takarar su 27.

Wannan na kunshe ne a cikin rahoton da kwamitin tantancewar ta gabatarwa kwamitin babban taron jam’iyyar karkashin jagorancin Gwamna Ahmadu Fintiri a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

2023: CAN ta yi gargaɗi kan tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki masu addini iri ɗaya

Babban taro: Jerin sunayen ‘yan takara 27 da PDP ta tantance domin zaben kwamitin ayyuka na kasa na jam'iyyar
Babban taro: Jerin sunayen ‘yan takara 27 da PDP ta tantance domin zaben kwamitin ayyuka na kasa na jam'iyyar Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Tsohon Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a, Mohammed Adoke ne ke jagorantar kwamitin inda tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Austin Opara, ke matsayin mataimakinsa.

A rahoton kwamitin, wanda aka kaddamar a ranar 23 ga watan Satumba, ya ce ya tantance ‘yan takara 32 inda biyu suka janye daga tseren, sannan kuma ta tantance mutum 27. Ta kuma ce ta ki tantance wasu ‘yan takara hudu.

Ga jerin sunayen yan takara 27 da kwamitin ya tantance:

1. Sanata Dr. Iyorchia Ayu

2. Amb. Umar Iliya Damagum

3. Hajiya Inna Maryam Ciroma

4. H.E. Amb Taofeek Arapaja

5. Prince Olagunsoye Oyinlola

6. Sen. Samuel Nnaemeka Anyanwu

7. Hon. Ahmed Yayari Mohammed

8. Hon. Umar Bature

9. Daniel Woyegikuro

10. Prof. Stella Effah-Attoe

11. Hon. Divine Amina Arong

Kara karanta wannan

Rigimar Shekarau da sauran masu fada da Gwamnoni ta kara jagwalgwalewa a APC

12. Muhammed Kakade Suleiman

13. Usman Elkudan

14. Kamaldeen Adeyemi Ajibade, SAN

15. Hon. Debo Ologunagba

16. Okechukwu Obiechina Daniel

17. Ikechukwu Samben Nwosu

18. Hon. Mrs. Chibuogwu Benson- Oraelosi

19. Hon. Arch. Setoji Kosheodo

20. Engr. Adedeji Doherty Engr. Adedeji Doherty

21. Ndubisi Eneh David

22. Alhaji Ibrahim Abdullahi

23. Sen. Chief Ighoyota

24. Hon. Adamu O. U. Kamale

25. Hajara Yakubu Wanka

26. Timothy Osadolor

27. Barr. Okechukwu Osuoha

Rikicin PDP na kara kamari yayin da ta hana wasu fitattun mambobi 3 tsayawa takara

A baya mun kawo cewa, kwamitin tantancewa na jam'iyyar PDP ya hana 'yan takara uku tsayawa takarar mukamai a kwamitin ayyuka na kasa na jam'iyyar.

Wadanda ba su cancanta ba da mukaman inji PDP sun hada da: Farfesa Wale Oladipo (Osun) wanda ya nuna sha’awarsa ga mukamin Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kudu.

Hakazalika da Okey Muo-Aroh (Anambra) wanda ya nuna sha’awar matsayin Sakataren Kasa Dakta Olafeso Eddy (Ondo) Sakataren Yada Labarai na Kasa na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Atiku zai iya gyara Najeriya: Gwamna ya bayyana gogewar Atiku da PDP a iya mulki

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng