Kano da sauran jihohi 7 da aka samu rabuwar kai a APC, aka zabi shugabanni 2 a jiha

Kano da sauran jihohi 7 da aka samu rabuwar kai a APC, aka zabi shugabanni 2 a jiha

Jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta gudanar da taron gangami na jihohi a ranar Asabar, 16 ga watan Oktoba, inda aka yi zaben shuwagabannin jam'iyyu na jihohi a fadin Najeriya.

Sai dai, jihohi da yawa sun ga sabon lamari tare da fitowar mambobi biyu na zartarwa yayin da jam’iyya mai mulki ke fafutukar ganin ta gyara gidanta kafin 2023.

A kasa mun kawi jerin jahohin da jam'iyyar APC mai mulki ta samar da wakilan zartarwa guda biyu sabanin daya da ya dace.

Kano da jihohi 7 da aka samu rabuwar kai a APC, aka zabi shugabanni 2 a jiha
Taron gangamin APC na jihohi | Hoto: All Progressives Congress - APC
Asali: UGC

1. Jihar Osun

A Osun, bangarori biyu na APC sun gudanar da taron gangamin don zaben sabon shugaban jam'iyyar, The Cable ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Da alamu dan tsagin Aisha Buhari zai ci zaben shugabancin APC a Adamawa

Bangaren da ke biyayya ga Gwamna Gboyega Oyetola an sake zabar Gboyega Famodun a matsayin shugaba.

A gefe guda kuma, bangaren da ke biyayya ga Rauf Aregbesola, tsohon gwamnan jihar kuma ministan harkokin cikin gida, an zabi Rasaq Salinsile a matsayin shugaban APC.

2. Jihar Legas

A Legas, Cornelius Ojelabi ya fito a matsayin shugaban jam'iyyar APC a jihar ta hanyar ittifakin. Sai dai kuma wani bangare mai suna Lagos4Lagos Movement ya zabi Sunday Ajayi a matsayin shugaban APC.

Hakanan a Legas, wani bangare da ake zargin yana biyayya ga tsohon gwamna Akinwumi Ambode ya samar da Beatrice Omotayo Tugbobo a matsayin shugaban APC, a cewar Sahara Reporters.

3. Jihar Kwara

A jihar Kwara, bangaren Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu, ya samar da Bashir Bolarinwa a matsayin shugaban APC.

A gefe guda kuma, bangaren da ke biyayya ga AbdulRahman AbdulRazaq, gwamnan jihar Kwara, sun zabi Sunday Fagbemi a matsayin shugaba.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda jami’an yan sanda suka tsere yayin da yan bindiga suka mamaye fadar sarkin Ogun yayin taron APC

4. Jihar Akwa Ibom

A bangaren da ke biyayya ga Godswill Akpabio, ministan harkokin Neja Delta, an zabi Steve Ntukekpo a matsayin shugaban APC.

A daya bangaren kuma, Austin Ekanem ya fito a matsayin shugaba a bangaren da Akpan Udoedeghe ke jagoranta, mukaddashin sakataren jam’iyyar APC na kasa.

5. Jihar Kano

A jihar Kano ta dabo kuwa, bangaren da Gwamna Abdullahi Ganduje ya amince da shi ya samar da Abdullahi Abbas a matsayin shugaba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai bangaren da Malam Ibrahim Shekarau ke jagoranta ya zabi Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban APC a wani taron na gangami na jihar.

6. Jihar Ogun

A jihar Ogun, bangaren masu biyayya ga Gwamna Dapo Abiodun sun zabi Yemi Sanusi a matsayin sabon shugaban jam'iyyar ta APC yayin da bangaren Ibikunle Amosun, tsohon gwamnan jihar, suka zabi Derin Adebiyi a matsayin shugaban APC.

7. Jihar Neja

Kara karanta wannan

Tsohon Kakakin majalisar dokoki da wasu jiga-jigai sun fice daga jam'iyyar APC, Zasu koma PDP

A jihar Neja, an kuma gudanar taron gangami a wurare biyu. Haliru Jikantoro ya fito a matsayin shugaban bangaren da Gwamna Abubakar Sani-Bello ya amince da shi yayin da wani bangaren kuma ya zabi Nasiru Ubandiya a matsayin shugaban APC na jihar.

8. Jihar Enugu

Batun bai sauya ba a jihar Enugu. Yayin da wani bangare ya samar da Adolphus Ude a matsayin shugaban APC, wani kuma ya samar da Ugochukwu Agballah.

PDP ta yi ittifaki kan Ayu Iyiorcha matsayin sabon shugabanta gabanin taron gangaminta

A bangaren PDP kuwa, jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Iyorchia Ayu ya zama dan takarar shugabancin jam'iyar PDP, gabanin babban taron ta na kasa na ranar 31 ga watan Oktoba.

Fitowar Ayu ya biyo bayan awanni na ci gaba da tarurrukan da masu ruwa da tsaki na PDP na Arewa ke yi a Abuja cikin awanni 72 da suka gabata.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: PDP ta tsayar da dan takarar shugabancinta gabanin babban taronta

An zabi Ayu ne bayan cin nasara kan wasu 'yan takara biyu; tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema da Sanata Abdul Ningi, inji Rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.