PDP ta yi ittifaki kan Ayu Iyiorcha matsayin sabon shugabanta gabanin taron gangaminta

PDP ta yi ittifaki kan Ayu Iyiorcha matsayin sabon shugabanta gabanin taron gangaminta

  • Jam'iyyar PDP ta yi ittfaki kan nadin sabon shugabanta gabanin taron gangami mai zuwa
  • An zabi Ayu Iyiorcha a matsayin sabon shugaban sabanin wasu 'yan takara biyu daga jihar Bauchi
  • Jam'iyyar PDP na shirin gudanar da taron gangamin jam'iyyar a karshen wannan watan na Oktoba

Abuja - Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Iyorchia Ayu ya zama dan takarar shugabancin jam'iyar PDP, gabanin babban taron ta na kasa na ranar 31 ga watan Oktoba.

Fitowar Ayu ya biyo bayan awanni na ci gaba da tarurrukan da masu ruwa da tsaki na PDP na Arewa ke yi a Abuja cikin awanni 72 da suka gabata.

DA DUMI -DUMI: Ayu ya zama dan takarar kujerar shugaban jam'iyyar PDP na kasa baki daya
Dakta Ayu Iyorchia | vanguardngr.com
Asali: UGC

An zabi Ayu ne bayan cin nasara kan wasu 'yan takara biyu; tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema da Sanata Abdul Ningi, inji Rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Da alamu dan tsagin Aisha Buhari zai ci zaben shugabancin APC a Adamawa

An tattaro cewa mataimakin shugaban PDP na kasa; Sanata Suleiman Nazif wanda zai tsaya a matsayin dan takara daya tilo daga yankin Arewa maso Gabas, ya gamu da cikas lokacin da Sanata Abdul Ningi, shima daga jihar Bauchi ya shiga jerin takarar.

A baya an dage taron masu ruwa na jam'iyyar ta PDP daga ranar Laraba zuwa Alhamis don ba da damar zabar Ayu a matsayin cikakken dan takarar shugabancin jam'iyyar ta PDP.

Wata majiya da ke da masaniya kan abin da ya faru a taron ta ce:

"Matsayin tattarawa na taron na da yawa kuma wadanda ke wurin sun shirya don jefa kuri'a amma gwamnoni sun san hakan don haka suka dage taron zuwa yau."

Bayan mika shugabancin PDP Arewa, an sanar da miliyoyi a matsayin kudin sayen fom

Kara karanta wannan

Hon Sha'aban: Da a yau za a yi zaben gwamna a Kano, warwas za a yi wa APC

A wani labarin, jam'iyyar PDP ta sanar da cewa, ta fara sayar da sayar da fom na tsayawa takarar mukaman shugabancin jam'iyyar, inda jam'iyyar ta bayyana farashin daban-daban ga mukamai na NWC, Vanguard ta ruwaito.

Yayin da fom din kujerar shugaban jam'iyya za ta kasance akan Naira miliyan 5, mataimakin shugaban jam'iyya da na sakatare na kasa za a sayar dasu a kan kudi Naira miliyan uku kowanne.

Fom din wasu ofisoshi a cikin NWC da suka hada da sakataren yada labarai na kasa, mai binciken kudi na kasa, sakataren kudi na kasa, shugaban matasa na kasa, ma’aji na kasa da mai ba da shawara kan harkokin doka, za su same shi a kan kudi naira miliyan biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.