Shehu Sani: Idan An Kasa Nuna Makarantun da Tinubu ya Halarta, An ga Wadanda Ya Gina

Shehu Sani: Idan An Kasa Nuna Makarantun da Tinubu ya Halarta, An ga Wadanda Ya Gina

  • Ana cigaba da cece-kuce kan batun rashin halartar makarantun firamare da sakandare na Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  • Sai dai, Sanata Shehu Sani yace ga wadanda basu san makarantun da ya halarta ba, ai sun ga wadanda ya gina a kasar nan
  • Sanatan ya bukaci jama'a su bar batun koda kuwa 'dan takarar shugabancin kasan ya gaza mika wa INEC shaidar makarantunsa

Rahotannin dake yawo kan cewa 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, bai mika takardun shaidar kammala karatun firamare sa sakandare ba ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, ya cigaba da janyo maganganu daga jama'ar kasar nan.

Mun kawo muku yadda Tinubu yayi ikirarin cewa wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun sace takardun makarantarsa a zamanin mulkin soja.

Kara karanta wannan

Jami'in INEC: Kuskure ne Ayyana Machina Matsayin 'Dan Takarar Sanatan Yobe ta Arewa a APC

Sanata Shehu Sani
Shehu Sani: Idan An Kasa Nuna Makarantun da Tinubu ya Halarta, An ga Wadanda Ya Gina. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Tsohon gwamnan jihar Legas ya sanar da hakan ne a wata takardar rantsuwa da ya kai wa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC a matsayin wani bangare na cike takardun takararsa ta zaben shugabancin kasa na 2023.

Takardun da aka saki ranar Juma'a sun nuna cewa Tinubu ya bar gurbin ilimin firamare da na sakandare ba tare da ya cike shi ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tinubu ya bayyana cewa ya samu digiri a harkar kasuwanci a 1979 a jami'ar Chicago.

A yayin martani kan lamarin a ranar Asabar a wallafarsa ta Twitter, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, yace ya dace a bar zancen nan idan har Tinubu bai samu kawo shaidar kammala karatutttukansa ba kamar yadda yayi ikirari.

"Jagaban ya gina makarantun firamare da sakandare; idan ka kasa gane wacce ya halarta, za ka iya ganin wacce ya gina kuna a bar zancen haka don Allah," ya wallafa a Twitter.

Kara karanta wannan

2023: 'Wasu Mutane Da Ba A Sanansu Ba' Ne Suka Sace Takardun Karatuna, Tinubu Ya Fada Wa INEC

Jam'iyya Zata Maka Tinubu a Kotu Kan Bayanan Bogi a Takardun Karatunsa

A wani labari na daban, jam’iyyar Action Peoples Party (APP) na shirin maka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu a gaban kotu don kalubalantar kwalin karatunsa.

Matakin ya biyo bayan zargin wasu kura-kurai a takardun karatun da Tinubu ya gabatarwa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Jaridar Leadership ta ruwaito.

Shugaban jam’iyyar ta APP, Uche Nnadi, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 24 ga watan Yuni, yana mai cewa jam’iyyar na da isassun hujojji a kan haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel