Da Dumi-Dumi: Bukola Saraki ya ziyarci Obasanjo kan batun takarar shugaban ƙasa a 2023

Da Dumi-Dumi: Bukola Saraki ya ziyarci Obasanjo kan batun takarar shugaban ƙasa a 2023

  • Tsohon gwamnan Kwara, Abubakar Bukola Saraki, ya isa gidan tsohon shugaban ƙasa Obasanjo kan batun takara a zaɓen 2023
  • Saraki, wanda rahotonni suka nuna yana can yana jiran Obasanjo, ya shirya gana wa da Deleget ɗin PDP a Sakatariyar jam'iyyar na Ondo
  • Hakan na zuwa ne bayan yunkurin da Saraki ya jagoranta na maslaha tsakanin yan takara ya ci tura

Ogun - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, ya isa gidan tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, dake Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Saraki, wanda ke neman takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar PDP, ya dira gidan Obasanjo ne dake harabar Laburarin sa (OOPL) da misalin ƙarfe 12:04 na tsakar rana yau Litinin.

Abubakar Bukola Saraki.
Da Dumi-Dumi: Bukola Saraki ya ziyarci Obasanjo kan batun takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa ya dira tare da yan tawagarsa da suka haɗa da tsohon shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Kawu Baraje, da sauran su.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka Saraki na can zaune yana jiran Obasanjo, wanda ya ke ganawar sirri da shuwagabannin Ibo.

Meyasa Saraki ya kai ziyara jihar Ondo?

Wakilin jaridar ya tattaro cewa tsohon shugaban majalisar Dattawan ya kai ziyara Ondo ne domin zawarcin Deleget ɗin PDP gabanin zaɓen fidda ɗan takarar PDP a zaɓen shugaban ƙasa.

Tsohon gwamnan jihar Kwara ya shirya gana wa da wakilan PDP a jihar bayan kammala tattauna wa da tsohon shugaban ƙasa Obasanjo.

Ɗan takarar ya shirya yin jawabi ga Deleget ɗin jam'iyyarsa ta PDP a Sakatariyar jam'iyya da ke Abeokuta.

Wannan na zuwa ne bayan yunkurin da Saraki ya jagoranta na haɗa kan yan takara da samar da maslaha a tsakanin su ya ci tura.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen Jaruman Kannywood da suka fito takara da kujerun da suke nema a 2023

A wani labarin na daban kuma Gwamnan APC ya bayyana babban abin da ya hana shi fallasa sunayen masu tallafawa yan bindiga a jihar Imo

Gwamna Uzodinma na jihar Imo ya ce hukumomin tsaro ne suka buƙaci karin lokaci shiyasa bai fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin yan bindiga ba.

Ya ce karo na karshe da suka tattauna sun bukaci ya ƙara musu mako biyu, bayan haka ya ce zai sanar da yan Najeriya sunan mutanen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel