Babban dalilin da yasa ban fallasa sunayen ma su rura wutar rashin tsaro a Imo ba, Uzodinma

Babban dalilin da yasa ban fallasa sunayen ma su rura wutar rashin tsaro a Imo ba, Uzodinma

  • Gwamna Uzodinma na jihar Imo ya ce hukumomin tsaro ne suka buƙaci karin lokaci shiyasa bai fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin yan bindiga ba
  • Ya ce karo na karshe da suka tattauna sun bukaci ya ƙara musu mako biyu, bayan haka ya ce zai sanar da yan Najeriya sunan mutanen
  • Wannan na zuwa ne a lokacin da yan bindiga ke cigaba da cin karen su babu babbaka a jihar Imo a baya-bayan nan

Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, a jiya Lahadi, ya ce babban abun da ya hana shi fallasa sunayen masu hannu a rashin tsaron Imo shi ne dan ya ba jami'an tsaro damar kammala bincike.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Legas, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.
Babban dalilin da yasa ban fallasa sunayen ma su rura wutar rashin tsaro a Imo ba, Uzodinma Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Furucin Uzodinma na zuwa ne a dai-dai lokacin da yan bindiga ke cigaba da cin karen su babu babbaka a Imo, inda suka kashe mutum biyu, suka fille wa ɗaya kai, suka yi garkuwa da wani.

Haka nan sun rubuta wa masu kasuwancin Man Fetur su tattara musu miliyan N20m matuƙar suna son cigaba da kasuwancin su a jihar, kamar yadda Tribune ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa gwamnan ya fasa faɗin sunayen a taron masu ruwa da tsaki?

Da yake amsa tambayoyin yan jarida, gwamna Uzodinma ya ce:

"Idan kuka duba taron masu ruwa da tsaki da muka yi a Owerri, wanda na shirya fallasa sunayen masu hannu a matsalar tsaro, a taron na ce hukumomin tsaro ne suka roki cewa saboda halin bincike ya yi wuri a faɗi sunayen kowa ya ji."

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

"Na yi gamsasshen bayani cewa zan bari su kammala aikin su. Karo na ƙarshe da na tuntuɓe su, sun buƙaci a ƙara musu mako biyu."
"Ina fatan nan da mako biyu komai zai kammala kuma zamu fallasa bayanan su ga duniya dan yan Najeriya su sani."

A wani labarin na daban kuma 'Yan bindiga sun halaka sama da mutane 50 a wani sabon mummunan hari a Zamfara

Yan bindiga sun sake kaddamar da wasu hare-haren ta'addanci kan al'umma a jihar Zamfara a ƙarshen makon nan

Bayanai sun nuna cewa yan ta'addan sun ƙashe akalla mutum 55 a yankunan kananan hukumomi biyu na jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel