An Yi Babban Rashi: Fitaccen Jarumin Fina Finan Bollywood, Dharmendra Ya Rasu
- Dharmendra Deol, fitaccen jarumin Bollywood, ya rasu a Mumbai yana da shekaru 89 bayan wata gajeriyar rashin lafiya
- An yi jana’izarsa a makabartar Pawan Hans, inda masoya suka yi jimamin rashin jarumin da ya fito a fina-finai sama da 300
- Jarumi Dharmendra, mahaifinsu Sunny ya yi fice a rawar Veeru da ya taka a shirin Sholay, tare da farin jini a barkwanci
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Mumbai - An yi babban rashi a masana’antar fina-finan Bollywood, yayin da fitaccen jarumin Indiya, Dharmendra Deol, ya koma ga mahaliccinsa.
Jarumi Dharmendra Deol, mahaifi ga su Sunny da Bobby Deol, ya rasu ne da safiyar Litinin a Mumbai yana da shekaru 89.

Source: Twitter
An yi jana’izar Dharmendra a Pawan Hans
'Yan sanda sun tabbatar wa jaridar The India Express cewa Dharmendra, wanda ya fito a fina-finai sama da 300, ya rasu ne bayan wata gajeriyar rashin lafiya da ya shafe akalla wata guda yana fama da ita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya nuna cewa an gudanar da jana’izarsa a makabartar Pawan Hans, yayin da jarumin da ake yi wa lakabi da He-Man na Bollywood ke shirin cika shekaru 90 a ranar 8 ga Disamba, 2025.
A watan Oktoba, 2025 ne aka kwantar da shi a asibiti saboda matsalar numfashi. Tawagarsa ta ce yana samun sauƙi, amma ya yanke shawarar ci gaba da zama a asibiti don samun kulawar likitoci sosai.
A farkon shekarar nan ma, an yi masa tiyatar ido, kuma har aka rika yada rahoton cewa ya rasu, amma daga baya aka karyata.
Dharmendra: Ɗan ƙauye da ya zama tauraron Bollywood
Dharmendra, wanda asalinsa ɗan ƙauyen Punjab ne, ya shigo harkar fim bayan ya lashe wata babbar gasar neman hazikan ‘yan wasa da wata mujallar fina-finai ta shirya.
Ya fara fitowa a fim ɗinsa na farko a 1960, Dil Bhi Tera Hum Bhi Tere, amma bai yi fice ba. Sai da ya fito a Shola Aur Shabnam a 1961 sannan ya fara haskakawa.
Jaridar The Times of India ta rahoto cewa jarumi Dharmendra ya kuma fito a fitattun fina-finai kamar:
- Anpadh (1962)
- Bandini (1963) — wanda ya ci kyautar kasa
- Phool Aur Patthar — wanda ya tabbatar da shi a matsayin jarumin fada
- Yaadon Ki Baraat, Pratigya, Chupke Chupke, Dream Girl, Sholay, da sauran su.
A tsawon tasirinsa, fina-finansa sun shafi barkwanci, soyayya, zuwa zazzafan fada. Rawar da ya taka ta Veeru a fim din Sholay ita ce mafi shahara har yanzu.
Abin da ake ji Dharmendra yake yawan fada shi ne:
"Ban samu lambobin yabo da yawa ba, amma soyayyar masoyana ita ce mafi girma."

Source: Twitter
Rayuwar soyayyar Dharmendra da iyali
A shekarun 1970, Dharmendra ya fara soyayya da fitacciyar jaruma Hema Malini yayin da suke haduwa a fim ɗinta na farko Tum Haseen Main Jawan.
Duk da yana da aure tun tuni da matarsa Prakash Kaur tare da ‘ya’yansa hudu — Sunny, Bobby, Ajeeta da Vijayta — soyayyarsa da Hema ta ci gaba da karfi.
Duk da kuma irin kalubalen da suka fuskanta na adawa daga iyalan Hema da jita-jitar za ta auri Jeetendra, sun dage sai da suka yi aure. Allah ya albarkace su da ‘ya’ya biyu — Esha da Ahana.
Bollywood: Jarumin barkwanci ya rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, fitaccen jarumin fina-finan Bollywood, Govardhan Asrani, ya rasu a ranar Litinin da rana bayan fama da matsalar numfashi.
Jarumin mai shekaru 84 ya rasu ne a Asibitin Bharatiya Arogya Nidhi da ke Juhu, Mumbai, inda aka kwantar da shi bayan likitoci sun gano taruwar ruwa a cikin huhunsa.
An gudanar da jana’izarsa a makabartar Santacruz da watan Oktoba, 2025, inda danginsa da abokansa na kusa suka halarta cikin sirri, kamar yadda ya bar wasiyya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


