Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 9 da sukayi aure tsakaninsu

Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 9 da sukayi aure tsakaninsu

Aure dai al'amari ne mai muhimmanci a rayuwar dan adam da akeyi saboda kaunar juna da hayayafa da kuma cika ka'idojin wasu addinai ko wasu dalilan daban. A yayinda wasu ma'auratan sukan hadu ne a wurare biki kamar aure, suna da sauransu, wasu na haduwa ne a wajen aiki kuma su shaku har su kai ga aure.

A yau dai Legit.ng ta kawo muku jerin sunayen wasu fitattun jaruman Bollywood guda 9 da suka sukayi aure tsakaninsu kuma har yanzu suna zaune tare kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

1) Amita Bachan da Jaya

Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu
Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu

A lokacin da ake shirya film din Zanjeer ne soyayya mai karfi ta shiga tsakanin jarumi Amita da Jaya a shekarar 1973 bayan gama shirya film din ne sukayi aure.

Sun sami 'ya'ya biyu a tsakanin su Abhishek Bachan da Shweta Bachan, shi Abhishek ya gaji mahaifinsa domin kuwa ya fantsama wajen harka fim.

Har yanzu suna tare duk da kasancewa Amita mai tsatstsauran ra'ayi.

2) Hema Malini da Dharmendra

Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu
Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu

Suma wasu fitattun jarumai ne da sukayi tashe a zamanin su, ana matukar ji da Hema saboda kyawunta.

A lokacin da Dharmendra ya kamu da soyayyar Hema yanada mata mahaifiyar Sony Deol inda ya nemi sakinta amma taki sai yace ai addinin musulunci ya yarje auren mace sama da daya sai kawai ya musulunta ya aureta a ranar 21 ga watan Agustan 1979.

3) Neetu Singh da Rishi Kapoor

Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu
Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu

Dukkan su sun fara fim ne tun suna yara. Inda suka zama aminan juna wanda Roshi baya iya boye mata sirrinsa.

Daga baya sai suka fuskanci sun kamu da son junansu. Ta karbi tayin soyayyar sa saidai anyi ta yamadidi dasu kasancewar bata isa aure ba.

Sun shafe shekaru biyar suna soyayya kafin suyi aure a 1980 lokacin tanada shekara 21.

4) Ajay Devgan da Kajol

Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu
Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu

Kajol da Ajay sun shafe shekaru Hudu suna soyayya kafin suyi aure duk da cewa akwai banbanci halayya a tsakanin su Wanda Kajol tana da faran faran da zolaya amma shi miskilini ne.

Ta fahimci halayyar sa shiyasa tasan yadda take tafiyar dashi har ta sashi dariya.

Sunyi aure a shekarar 1999 wanda Har yanzu suna tare akwai yara biyu a tsakanin su.

5) Aishwarya Rai da Abhishek Bachan

Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu
Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu

Abhishek ya bayyanawa Aishwarya kudirin sa na sha'awar auren ta wanda ta nuna amincewar ta. Sunyi aure a shekara ta 2017.

Duk da cewa ta girme masa da shekara biyu suna zaune lafiya tare da yarinyar su guda daya.

6) Twinkle Khanna da Akshay Kumar

Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu
Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu

Khanna tace bata taba jin dadi a harkar fim ba sai da ta hadu da Akshay.

Sunyi aure a 2001 sun sami 'ya'ya biyu suna zaune lafiya. Yanzu haka Khanna ta ajjiye fitowa a fina-fina.

7) Kareena Kapoor da Saif Ali Khan

Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu
Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu

Kareena jaruma ce ta akeji da ita, duk da cewa Saif ya taba aure harda yara biyu hakan bai hanata tsumduma cikin soyayyar sa ba.

Bayyanar soyayyar su a 2009 ta baya kowa mamaki inda sukayi aure a shekarar 2012.

Dukkaninsu sunci gaba da fitowa a fina-fina sannan akwai fahimtar juna tsakanin Kareena da 'ya'yan mijinta.

8) Genelia da Ritesh Deshmuek

Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu
Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu

Sun kasance aminan juna wanda daga baya amintar takoma soyayya .

Sunyi aure a shekarar 2012 wanda yanzu haka suna da yara biyu..

9) Soha Ali khan da Kunal Khemu

Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu
Bollywood: Fitattun jaruman Indiya 8 da sukayi aure tsakaninsu

Sun hadu ne a lokacin da ake shirya wani fim, wata alaka bata taba shiga tsakanin su ba face ta fim amma daga baya komai sai ya canja.

Sun dade suna soyayya kafin suyi aure a shekarar 2015.

Yanzu haka suna da diya guda daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel