9ice: An Yi wa Fitaccen Mawaƙin Najeriya Sihiri, Ya Shafe Watanni 6 Yana Aman Jini
- Mawaki 9ice ya bayyana cewa an yi masa sihiri mai tsanani a 2010 inda ya kwashe wata shida yana ama jini ba tare da waraka ba
- Ya ce sai da aka kai shi wurin Babalawo sannan ya samu sauki, wanda hakan ya sa ya rungumi addinin gargajiya ka'in da na'in
- A wata hira da Nancy Isime, 9ice ya bayyana cewa shedan ne ke jan ragamar masana’antar waka, kuma mawaka na karkashinsa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Fitaccen mawaki, Alexander Akande, (9ice), ya bayyana yadda ya fuskanci mummunar matsala ta sihiri da ta kusa hallaka shi a shekarar 2010.
Mawaki 9ice ya bayyana cewa ya kwashe tsawon watanni shida yana aman jini ba tare da likitoci sun gano abin da ke damunsa ba.

Kara karanta wannan
Bayan bidiyon Ummi Nuhu, Mai Dawayya ya yi tone tone, ya faɗi shura da ya yi a baya

Source: Instagram
Yadda aka yi wa mawaki 9ice sihiri a 2009
A cikin wani shirin talabijin na jaruma Nancy Isime, 9ice ya ce cutar da ta same shi ba ta asibiti ba ce, illa sihiri wanda ya shawo kansa daga magungunan malaman gargajiya.
Ya ce sai da aka kai shi wurin Babalawo (wani bokan Ifa), sannan ya samu waraka, lamarin da ya sa ya rungumi addinin gargajiya ka'in da na'in.
Mawaki 9ice ya ce:
“Ni ba Kirista ba ne, ba Musulmi ba ne – ni Babalawo ne. Ni Ba'afrike ne. Ni mai bin addinin gargajiya ne. Na fara sanin Ifa ne lokacin da nake aman jini.
"Wani ne ya kai ni wurin Ifa. Ina nadamar rashin sanin Ifa tun farko. Fela yana zuwa wurin Ogun (wanda 'yan addinin gargajiya ke bautawa), mutane na masa dariya, amma yanzu na fahimci dalilinsa.”
'Shedan ke jan ragamar masana'anta waka'
A yayin tattaunawar, Nancy Isime ta tambaye shi ko ya taba fuskantar gwagwarmayar sihiri a rayuwarsa ta waka, sai 9ice ya amsa da cewa hakan ya faru sau da dama.

Kara karanta wannan
Amnesty Int'l ta dura kan Tinubu da gwamnati ta ƙi tsoma baki shekaru 6 da 'sace' Dadiyata
Ya kara da cewa mafi muni cikin su shi ne lokacin da ya kwashe watanni shida yana aman jini a gidansa a shekarar 2009/2010, wanda daga bisani ya tilasta masa barin gidan gaba daya.
Mawakin ya kuma fito baro baro yana cewa shedan ne ke jan ragamar masana'antar nishadi, musamman waka, inda ya ce mawaka ne 'yan amshin shedan.
"Shedan ne ke jan ragamar masana'antar waka, shi ne ke uban gayya a komai."
- Mawaki 9ice.

Source: Instagram
Tarihin rayuwar mawaki 9ice
Alexander Abolore Adegbola Akande, wanda aka fi sani da 9ice, mawaki ne kuma marubucin wakoki daga Najeriya, wanda aka haife shi a ranar 17 ga Janairu, 1980 a Ogbomosho, jihar Oyo.
Ya taso a Bariga da ke Lagos, kuma ya samu karbuwa sosai a tsakiyar shekarun 2000 bayan fitar waƙar Gongo Aso a 2008, wadda ta zama waka mai tasiri a Najeriya da ma waje.
Wasu daga cikin fitattun kundin wakokinsa sun hada da Certificate (2007) da Gongo Aso (2008), wadanda suka tabbatar da shi a matsayin jagoran wakokin afrobeats a harshen Yarbanci.
Kalli wani bangare na tattaunawar a nan kasa:

Kara karanta wannan
Cin amana: Magidanci ya kama matarsa tsirara da wani namiji a gado, ya ɗauki mataki
An kama mai cire sassan matattu a makabarta
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar 'yan sandan Lagos ta kama wani matashi dauke da sassan jikin mutum a cikin jakarsa a yankin Epe.
Wanda ake zargin ya ce ya tono sassan ne daga kaburbura a Edo da kuma gawarwakin mutanen da suka rasu a hadura.
Rundunar 'yan sandan Lagos ta ce an kama matashin ne yana kokarin kai sassan jikin ga boka domin yin tsafi don samun kudi.
Asali: Legit.ng