Mazauniya Kaduna: Aman jini na dinga yi bayan anyi min riga-kafin korona

Mazauniya Kaduna: Aman jini na dinga yi bayan anyi min riga-kafin korona

- Wata mata mai zama a Kaduna ta bada labarin yadda ta dinga fitar da jini ta baki da hanci bayan an yi mata allurar korona

- Bidiyon da wata mata mai suna Hannatu Tanko ke bayani ya karade kafafen sada zumuntar zamani

- Duk da asibitin da taje sun barranta kansu daga wannan ikirarin, ta ce a cikin garin Kaduna taje ta karba allurar

Wata mazauniya jihar Kaduna mai suna Hannatu Tanko ta bada labarin yadda jini ya dinga fita ta baki da hancinta bayan an yi mata riga-kafin cutar korona.

A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, matar wacce ta je neman lafiya a asibitin kwararru na Ashmed dake Kaduna ta bada labarin abinda ta fuskanta.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, duk da matar da bakinta tace an yi mata allurar riga-kafin a sakateriyar karamar hukumar Kaduna ta kudu, mutane da yawa sun alakanta hakan da asibitin.

KU KARANTA: Auren mace fiye da daya yana habaka tattalin arziki, Biloniya Ned Nwoko

Mazauniya Kaduna: Aman jini na dinga yi bayan anyi min riga-kafin korona
Mazauniya Kaduna: Aman jini na dinga yi bayan anyi min riga-kafin korona. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kutsa sansanin sojoji a Niger, sun sheke wasu dakarun

Domin nisanta kansu daga lamarin, shugaban asibitin, Dr Patrick Echobu, yayi jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis.

Ya ce matar ta zo asibitin bayan kwanaki shida da aka yi mata riga-kafin a wani wuri na daban.

Shugaban asibitin yace, "A madadin asibitin kwararru na Ashmed, muna nisanta kanmu tare da kushe bidiyon da wata majinyaciya ke yadawa. Ta bayyana kanta a ranar 30 ga watan Maris cewa tana aman jini ta baki da hanci.

"Mun karbeta bayan kwanaki shida da ta yi riga-kafi amma bamu san lokacin da ta fara yi wa jama'a bayani ba har aka dinga yadawa a kafafen sada zumunta.

"Muna so mu sanar da cewa bamu da alaka da abinda ke yaduwa. Ina farin cikin sanar da cewa ma'aikatanmu sun yi riga-kafin."

A wani labari na daban, 'yan sanda sun damke wani da ake zargin yana da alaka da harin da aka kaiwa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Farfesa Charles Soludo, a jihar Anambra.

Channels TV ta ruwaito cewa, Ikenga Tochukwum, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis.

Farfesa Soludo, wanda shine yake son fitowa takarar kujerar gwamnan jihar Anambra, ya halarci taron masu ruwa da tsaki da wasu 'yan siyasa a karamar hukumar Aguata dake jihar.

Source: Legit

Online view pixel