Soshiyal Midiya Ta Ɗauki Zafi: G Fresh Alameen Ya Auri Wata Fitacciyar Ƴar TikTok

Soshiyal Midiya Ta Ɗauki Zafi: G Fresh Alameen Ya Auri Wata Fitacciyar Ƴar TikTok

  • Bidiyon auren G-Fresh Alameen da Alpha Charles Borno suna rungumar juna ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta
  • Sama da mutane miliyan 1 sun kalli bidiyon, inda wasu suka taya 'yan TikTok din murna yayin da wasu suka soki auren
  • Auren G-Fresh da Alpha Charles ya jawo ka-ce-na-ce musamman saboda ganin Alpha Kirista ce kuma kawar Sadiya Haruna

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kafafen sada zumunta sun dauki zafi yayin da aka samu bullar bidiyon auren fitaccen dan TikTok na Arewa G-Fresh Alameen da Alpha Charles Borno.

G Fresh da Alpha Charles sun yi kaurin suna a dandalin TikTok, wanda ya sa ganin bidiyonsu suna rungumar juna ya jawo ce-ce-ku-ce mai zafi.

Mutane sun yi tsokaci yayin da G-Fresh Al-ameen ya auri Alpha Charles Borno
Alpha Charles Borno ta yi wuff da fitaccen dan TikTok, G-Fresh Al-Ameen. Hoto: gfresh_alameen
Asali: Instagram

G-Fresh da 'yar TikTok sun sun yi aure

A bidiyon da shi G Fresh ya wallafa a shafinsa na Instagram, an ga 'yan TikTok din suna rungumar juna sanye cikin fararen kaya.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali: Bello Turji ya kafa sabon sansanin ta'addanci a jihar Sokoto

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alpha Charles Borno wacce Kirista ce tana sanye da kaya irin na amare wanda ya sa ake kyautata zaton cewa bidiyon na bayan aurensu ne.

G-Fresh Alameen ya rubuta "Ina sonki" a jikin bidiyon da ya jawo sama da mutane 80 suka yi tsokaci a kan shi, yayin da sama da 1,000 suka nuna alamar kauna a kansa.

Bidiyon G-Fresh da Alpha Charles ya yadu

Da Legit Hausa ta leka shafin Alpha Charles, an ga 'yar TikTok din ta dora bidiyonta da G-Fresh Al-Ameen tare da kiransa da "Mijina."

Sama da mutane miliyan daya suka kalli wannan bidiyo na Alpha Charles yayin da sama da mutane 12,000 suka yi tsokaci a kanshi.

Da yawa daga cikin wadanda suka yi tsokaci a kan bidiyon, sun nuna mamakin wannan auren na 'yan TikTok din biyu, ganin cewa dukansu sun yi kaurin suna a dandanlin.

Abin da mutane ke cewa kan auren G-Fresh

Kara karanta wannan

An kona makarantar Kandahar a Bauchi: Rigima ta kaure tsakanin matasa da ƴan CJTF

Mun tattaro kadan daga ra'ayoyin mutane kan auren G-Fresh da Alpha Charles.

Maska2:

"Ba haramun ba ne Musulmi ya auri Kirista, sai dai haramun ne Musulma ta auri Kirista. Allah ya ba ku zaman lafiya, kude na ma abun mummunar fahimta."

0fficial_Abbaxup🎸😃:

"Wannan masifa da take faruwa a TikTok Allah ya kawo mana karshenta."

Sadee-ngaski_collection:

"Ni gaba daya sun goge min hadda na rasa abun fadi"

beenta_uba:

"Ban taba shiga cikin mamaki ba wallahi tunda na fara TikTok sai yau. Abun fadan ma bansan ta ina zan fara ba. Ikon Allah."

faisalco_bdc:

"Kai anya kuwa ba G Fresh ba ne Judal da zai zo karshen zamani?"

Abubakar Saleh297:

"Sakarai, sai dai mata masu kudi su aureka da sun gai su sake ka."

samrat19.com:

"Ubangiji ya sa idan kun yi mutuwane za ta raba ku, ubangiji ya bawa Alpha ikon karban Musulunci."

maryamladan003:

"To miye wannan haukar duk a kan Sayyada har za ka auri wadda ba Musulma ba, ita kan Sayyada ta yi gaba. Wallahi ku ta bari da hauka a kan ta."

Kara karanta wannan

Jarumar Kannywood, Bilkisu ta saki sababbin hotuna da suka bayyana surar jikinta

Sadiya Haruna ta maka G-Fresh a kotu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sayyada Sayadiya Haruna ta maka fitaccen dan TikTok na Arewa, G-Fresh Al-Ameen a gaban kotu, inda take neman a raba aurensu.

Sadiya Haruna wadda ta yi ikirarin cewa ita ce ta dauki nauyin aurensu gaba daya, ta shaidawa kotun cewa ta gano G-Fresh ba kalar namijin da za ta yi zaman aure da shi ba ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.