Sadaki da Kayan Lefe Sun Yi Tsada, An Gano yadda Maza Ke Raba Kafa a Neman Aure

Sadaki da Kayan Lefe Sun Yi Tsada, An Gano yadda Maza Ke Raba Kafa a Neman Aure

  • Tsadar rayuwa da ake fama da ita ta fara horar da maza musamman wadanda ke shirin yin aure, yanzu suka fara raba kafa a soyayya
  • An ce yanzu maza sun koma soyayya da 'yan mata da dama, kuma su nemi matan su basu kiyasin kudin da za su kashe a lokacin aurensu
  • Maza kan auna dogon burin mace ko rashin son kudinta wajen tantance wanda za su iya aura, domin gudun kashe kudin da ya fi karfinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A cikin 'yan shekarun nan, an samu sauye sauye a al'adar aure, wanda ya hada da sauyi na zamantakewa, tattalin arziki da kuma canjin muradan jama'a.

An samu bullar wani bakon al'amari, inda maza ke jinkirta kai kudin aure har sai sun fara tambayar budurwa hasashenta na kudin da za su kashe a bikin auren.

Kara karanta wannan

Raba kasa: Dattijon Arewa, Tanko Yakasai ya hango makomar Najeriya

Rahoto ya yi magana kan yadda tsadar rayuwa ta shafi yadda maza ke neman aure
Rahoto ya nuna yadda maza suka koma raba kafa wajen neman aure saboda tsadar rayuwa. Hoto: Ariel Skelley
Asali: Getty Images

Hikimar hakan ita ce; namiji zai gane macen da ke da dogon buri da son kyale-kyale domin ba shi zabi na ya aure ta ko ya nemi wata tun wuri, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Neman aure: Maza sun fara raba kafa

Rahoto ya nuna cewa, akwai mazan da ke zuwa wajen mata daban daban, su bukaci matan su ba su jadawalin dukkanin abubuwan da suke bukata na aurensu.

Mazan kan zauna, su duba kudin da za su kashe na auren 'yan matan, a ciki ne za su zabi wanda kudin aurenta ya zamo mafi araha, da nufin gudun kashe kudi.

Wannan bakon al'amari da ya samo asali daga tsadar rayuwa da ake ciki, ya haifar da tambayoyi masu yawa kan nagartar soyayya da kuma iyakance aure kan dalili daya.

Yayin da maza ke kokarin gujewa auren mace 'yar karya ko a ce mai son kudi da aljihunsa zai jigata wajen aurenta, da yawa na ganin akwai yaudara a raba kafar da mazan ke yi.

Kara karanta wannan

Tattalin arziki: Gwamnati ta fadi yadda za a hana Dala tashi kan Naira

Me ake sanyawa a lissafin kayan aure?

Al'adar aure ce namiji ya kashe kudi a yayin da zai auri mace. Sau tari, maza da mata kan rubuta dukkanin abubuwan da suke da bukatar yi a lokacin aure.

Lissafin aure a wajen maza na farawa ne tun daga farkon soyayya, irin kyautar da samari ke yi wa 'yan mata, sannan azo batun kai kudin na gani ina so, zuwa hada lefe da biyan sadaki.

Kashe kudi a aure na da nasaba da gari, kabila, al'ada da kuma wadata. Akwai macen da za ka kashe sama da Naira miliyan daya, wata ko N500,000 ba za ka kashe ba.

Maza kan auna wadatar gidansu yarinya, ko yanayin yadda ta nuna masa son kudi (dogon buri) ko kuma yanayin tattalin arziki kafin ya yanke hukuncin wanda zai aura.

N142,000: Sadakin aure ya kara tsada

A wani labarin, mun ruwaito cewa kwamitin ganin wata na kasa ya sanar da cewa sadakin aure ya koma N141,932 wanda kuma daidai yake da haddin yin sata.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare babbar hanya, sun kashe matafiya, an sace wasu da dama

Kwamitin ya fitar da jadawalin kudaden a ranar 17 ga watan Rabi’ul Awwal, 1446 (Hijira) wanda ya yi daidai da 20 ga watan Satumbar 2024 (Girigoriya).

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.