Matsaloli 5 da ke hana 'yan mata samun mazan aure da wuri

Matsaloli 5 da ke hana 'yan mata samun mazan aure da wuri

Rashin aure da wuri a wannan zamani na daya daga cikin matsalolin da ke ci wa al'ummar mu tuwo a kwarya musamman ma a tsakanin mata wadan da yanzu kan dade basu samu mijin aure ba.

Sai dai duk da alkaluman da ke nuna cewa mata a wannan zamanin na neman su fi maza yawa, masana na ganin akwai wasu dalilai da dama da ke sa matan yin nauyin kasuwa.

Matsaloli 5 da ke hana 'yan mata samun mazan aure da wuri
Matsaloli 5 da ke hana 'yan mata samun mazan aure da wuri

KU KARANTA: 'Yan Najeriya za su sha ruwan kudi bayan lallasa kasar Iceland

Legit.ng ta samu ta tattaro maku wasu daga cikin manyan dalilan da aka fi danganta su da alhakin kawowa matan cikas.

1. Ruwan ido: Wasu matan dai ruwan ido gare su. Za kuji cewa su suna cewa sai mai kudi iri kaza da mota kaza ko gida kaza.

2. Zurzzurfan karatu: Maza da dama dai na tsoron auren macen da tayi nisa sosai a karatun zamani suna ganin cewa ba za su iya juya ta ba.

3. Zafin kishi: Wasu matan suna da zafin kishi shi ne ma ya ke sanyawa kuji sunce ba su son mai mata koda kuwa shi yana da sha'awar auren su.

4. Tsadar al'adun aure: A lokuta da dama dai mata da maza dukan su kan dade basu yi aure ba sakamakon tsananin tsadar al'adun da aka likawa auren kamar su kayan daki da lefa da sauran bidi'oi.

5. Sihiri: Wasu matan kan dade a gidajen iyayen su ne ba aure a sanadiyyar sihirin da wasu makiya ko mahassadan su kan yi masu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng