Bidiyo: Naziru Sarkin Waka Ya Yi Askin Kwal Kwabo, Ya Roki Mutane Ka da Su Yi Dariya

Bidiyo: Naziru Sarkin Waka Ya Yi Askin Kwal Kwabo, Ya Roki Mutane Ka da Su Yi Dariya

  • Fitaccen mawakin sarauta, kuma sarkin wakan sarkin Kano, Naziru M. Ahmed ya saki bidiyon sabon askin da ya yi na 'kwal kwabo'
  • Sama da mutane 1,000 suka tofa albarkacin bakinsu kan wannan aski da Naziru ya yi inda ya yawa suka yi dariya tare da jinjina masa
  • Mawakin dai ya roki masu bibiyarsa da ka da su yi dariya idan sun kalli bidiyon, amma wani ya ce "ko dai daga ofishin Hisbah ka fito?"

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Naziru M. Ahmad, sarkin wakan sarkin Kano ya sake jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan da ya saki bidiyon sabon askin da aka yi masa na 'kwal kwabo.'

Kara karanta wannan

"Na gano mafita," Sarki Sanusi II ya shirya kawo karshen rikicin Fulani a Najeriya

Kamar yadda aga gani a cikin bidiyon, wanzamin da ya yi askin ya kware a aikinsa domin saman kan mawakin har wani sheki ya ke yi saboda ya salsale shi 'tal'.

Mawaki Naziru M. Ahmad ya yi sanom askin kwal kwabo.
Naziru ya saki bidiyon sabon askin kwal kwabo da ya yi, mutane sun yi dariya. Hoto: sarkin_wakar_san_kano
Asali: Instagram

Naziru ya yi askin kwal kwabo

Naziru sarkin waka ya wallafa bidiyon a shafinsa na Instagram. A cikin bidiyon an ga mawakin a gaban wani madubi yana sauraron wakar da ya yi ta 'Tawa'.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganin mawaki Naziru yana bin wakar tare da yin rangaji da kai, yayin da kuma ya yiwa kansa askin 'kwal kwal' zai tabbatar maka yana cikin nishadi a lokacin.

Mawakin ya rubuta cewa:

"Nayi talliya ne, dan Allah ban da dariya!"

Askin Naziru ya jawo magana

Daga lokacin da mawakin ya wallafa wannan bidiyo zuwa lokacin da muka wallafa wannan rahoto, sama da mutane 1,000 ne suka yi magana.

Kara karanta wannan

An gano bidiyon Bello Turji yana shan alwashi bayan kwace motocin sulken sojoji

Legit Hausa ta tattaro kadan daga cikin abin da masu bibiyar mawakin suka ce kan wanna askin da ya yi:

fulata_mahre:

"Sunan wani gari wai Jama'are."

iam_abubakar_siddiqi:

"Anya ba daga ofishin Hisbah ka fito ba?"

sarkin_yakin_sarkin_waka:

"Wallahi har ka kara kyau shugaba."

kabiru_father_ambursa:

"Dariya kam sai mun yi dariya oga."

aishadaraja:

"Ka saukewa kan aljanu, ba su da wajen zama yanzu."

miss_khairy:

"Har na tuna da kakana Talle."

bin_sule1:

"Mama ta tace wallahi sarki ka yi kyau, ka yi kiba sai ka kara zama baban mutum."

Kalli bidiyon a nan kasa:

Naziru ya caccaki 'yan kirifto

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen mawakin Arewa, Naziru Sarkin Waka ya caccaki 'yan kirifto musamman wadanna ke harkar 'minning' inda ya kira abin da "bata lokaci."

A yayin da matasa ke jiran fashewar Tapswap, Naziru sarkin waka ya ce maimakon jiran abin da ba shi da tabbas, kamata ya yi matasan su kama sana'a ta dahir.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.