Karamar sallah: Hotunan wankan sallah na Naziru sarkin waka da iyalinsa

Karamar sallah: Hotunan wankan sallah na Naziru sarkin waka da iyalinsa

  • Jama'a na ci gaba da gudanar da shagulgulan bikin karamar sallah cikin annashuwa da walwala
  • Ba a bar shahararren mawakin nan na Kannywood, Naziru sarkin waka ba a baya inda ya yi wanka na kece raini tare da iyalinsa
  • A hotunan da ya wallafa a shafukinsa na sadarwa, an gano shi tare da yaransa mata biyu da namiji daya

Shahararren mawakin nan na Kannywood, Naziru Ahmad Sarkin Waka ya yi bikin karamar sallah tare da iyalinsa.

Mawakin ya saki wasu zafaffan hotunansa tare da yaransa a yayin da ake ci gaba da shagulgulan sallah na wannan shekarar.

Karamar sallah: Hotunan wankan sallah na Naziru sarkin waka da iyalinsa
Karamar sallah: Hotunan wankan sallah na Naziru sarkin waka da iyalinsa Hoto: sarkin_wakar_san_kano
Asali: Instagram

A kasan hotunan da ya wallafa a shafinsa na Instagram mai suna sarkin_wakar_san_kano ya rubuta ‘Nera da jini… #sallah #day2’.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mabiyansa sun yi masa fatan alkhairi

ymd3_official ya yi martani:

"Fariyar mu danmu namiji Allah ya raya #Sarki jr"

hannysuu ya ce:

"Allah ya shiryar maka dasu"

algoniarab ya rubuta:

"Dan Almajiri"

beeeman619 ya ce:

"Dauka ka daga Allah neh‍♂️"

A baya-bayan nan ne sarkin waka ya shiga takaddama da abokan sana’arsa bayan ya jefe su da zargin aikata lalata.

Lamarin ya kai ga har sai da jaruman masa’antar Kannywood da dama suka fito suka yi masa raddi.

Kalaman Sarkin Waka: Mun yi dawafi a kanka, mun hada ka da Allah, Jarumai maza a Saudiyya

A gefe guda, mun ji cewa batun rigimar Sarkin Waka da Nafisa Abdullahi, duk da dai wadanda suka fara rigimar sun yi shiru, wasu daga cikin 'yan masana'antar shirya fim basu bar maganar ba.

Kara karanta wannan

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

Har yanzu a nan da chan ana dan jin maganganu da rubuce-rubuce na nuna rashin jin dadin abinda sarkin wakan ya yi ga 'yan uwansa 'yan fim yayin da magoya bayansa na nasu rubutun musamman a Facebook da tiktok.

Yayin da mafi yawan 'yan kannywood da suka halarci Saudiyya suka ki tofa nasu albarkacin bakinsu suka mayar da hankali kan ibadunsu, Malam Ibrahim Sharukhan, Sani Candy, Suleiman Costume da mai haska dandali kuma jarumi Adebo, sun bayyana cewa sun yi dawafi kuma sun kai karar Naziru wurina Allah kan abinda yake musu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel