An Shiga Alhini Bayan Sanar da Rasuwar Fitaccen Jarumin Fina Finai a Najeriya

An Shiga Alhini Bayan Sanar da Rasuwar Fitaccen Jarumin Fina Finai a Najeriya

  • An shiga jimami bayan sanar da rasuwar fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Yusuf Olorungbede a jiya Talata
  • An sanar da rasuwar marigayin ne a shafukan sada zumunta wanda aka bayyana da mutum mai son taimakon jama'a
  • Fitacciyar jarumar fim a Nollywood, Foluke Daramola ta shaidawa duniya rasuwar Yusuf a shafinta na Instagram

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Fitaccen jarumin fina-finai a masana'antar Nollywood ya riga mu gidan gaskiya a jiya Talata 27 ga watan Agustan 2024.

Marigayin mai suna Yusuf Olorungbede ya rasu ne bayan fama da jinya na tsawon lokaci wanda ya yi ajalinsa daga karshe.

Jarumin fina-finai a Nollywood ya kwanta dama
An sanar da rasuwar fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Yusuf Olorungbede. Hoto: @olorungbebeyusu.
Asali: Instagram

Jarumin fina-finan Nollywood, Yusuf ya rasu

Kara karanta wannan

Nuhu Ribaɗu ya yi babban rashi, Allah ya yiwa surukarsa rasuwa a Abuja

Jarumar fina-finai, Foluke Daramola ita ta sanar da rasuwar marigayin a shafinta na Instagram a jiya Talata 27 ga watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abokan sana'arsa da dama sun yi jimamin mutuwar jarumin inda suka bayyana shi a matsayin mutumin kirki.

Har ila yau, magoya bayan jarumin da sauran jaruman masana'antar Nollywood sun bayyana kaduwarsu a shafukan sada zumunta daban-daban.

Jarumar fina-finai ta godewa al'umma kan gudunmawarsu

A cikin sanarwar da Daramola ta fitar, ta yi jimamin rashin inda ta yi godiya ga al'umma da suka yi musu ta'azziya da kuma gudunmawa da suka bayar.

"Mun yi rashin Yusuf Olorungbede, mun mika dukan lamuranmu ga Ubangiji mahalicci, muna godiwa ga al'umma gaba daya."

- Foluke Daramola

Kafin rasuwar Yusuf, Foluke ta nemi taimakon yan uwa da abokan arziki inda ta gode musu game da gudunmawar da suka bayar.

Kara karanta wannan

Ambaliya: An gano adadin wadanda su ka mutu da rasa muhallansu a jihohin Arewa 3

Fitacciyar mawakiyar yabo ta kwanta dama

A wani labarin, kun ji cewa an shiga jimami bayan sanar da rasuwar fitacciyar mawakiyar yabo na addinin Kirista bayan fama da jinya.

An sanar da labarin rasuwar marigayiya Aduke Ajayi da aka fi sani da Aduke Gold ne a ranar Litinin 12 ga watan Agustan 2024.

Wata majiya ta tabbatar da cewa mawakiyar da aka fi sani da Gold ta rasu ne a ranar Litinin a asibitin koyarwa da ke Ibadan a jihar Oyo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.